Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta sake duba tsarin gine-ginen birnin Maiduguri domin rage illar ambaliya a babban birnin jihar.
Zulum ya bayyana hakan ne bayan ya kammala duba ayyukan gyaran da ake gudanarwa a madatsar ruwan Alau, inda ya nuna damuwa kan yadda wasu mazauna birnin ke gina gidaje a kan hanyoyin ruwa da kuma zubar da shara a cikin magudanan ruwa.
Za mu fara sake duba tsarin gine-ginen birnin domin tabbatar da cewa dukkan magudanan ruwa da hanyoyin ruwa sun kasance masu aiki,” in ji Gwamna Zulum.
Ya gargadi jama’a cewa duk wani gini da aka kafa a kan hanyar ruwa zai fuskanci rushewa domin kaucewa sake faruwar ambaliyar da ta afku a ranar 10 ga Satumba, 2024, a yankin Maiduguri da Jere.
“Kungiyoyin injiniyoyinmu da naku su hada kai don fitar da ingantaccen shiri da zai hana sake afkuwar abin da ya faru a baya,” in ji shi.
Yayin da yake duba ci gaban aiki a madatsar ruwan Alau, Zulum ya bayyana cewa akwai fargaba a tsakanin mazauna Maiduguri game da yiwuwar sake afkuwar ambaliya.
Sai dai ya kwantar da hankulan jama’a kan hauhawar ruwa a madatsar ruwan, inda ya bayyana cewa bisa binciken injiniyoyi “babu wani abin tsoro”.
Zulum ya bayyana cewa wani dan kwangila ya bayyana damuwa kan yawan ruwa, lamarin da ya sa gwamnatin jihar ta dauki matakin gaggawa.
Ya yabawa dan kwangilar bisa kokarinsa da sa ido kan matakin ruwa, sai dai ya ja hankali da cewa, “Ina ba da shawarar mu yi taka-tsantsan; mu kasance a gefen kariya, la’akari da yadda dumamar yanayi ke kara kamari a duniya.”
Bayan ya saurari jawabin dan kwangilar, Gwamna Zulum ya nuna bukatar kara tsawon lokacin aikin, yana mai cewa, “Muna bukatar wannan karin da kuka ambata, domin ba mu san abin da zai faru gobe ba.”
Karin aikin na nufin gina wani sabon bangare ne domin karbar karin ruwa da zai iya haifar da ambaliya.
“Kungiyoyin injiniyoyinmu da naku su hada kai don samar da sahihan shawarwari da za su tabbatar da cewa abin da ya faru a baya ba zai sake faruwa ba,” in ji shi.
A tuna cewa gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 80 a watan Maris domin sake gina gine-ginen da ambaliya ta lalata da kuma kara wasu sabbin gine-gine a madatsar ruwan Alau.



