Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa mata da yara ne suka fi shan wahala a ambaliyar da ta afku a shekarar 2025 a jihohi 19 na Najeriya.
Wannan bayani na kunshe ne a cikin sabuwar kididdigar da hukumar ta wallafa a dandalinta na bayanai a ranar Juma’a, inda ta bayyana cewa an samu asarar rayuka 165, mutane 82 sun ɓace, yayin da mutane 119,791 suka shafa gaba ɗaya.
Jihohin da suka fi fuskantar tasirin ambaliyar sun hada da Imo, Rivers, Abia, Borno da Kaduna, bisa ga bayanan da NEMA ta fitar.
Hukumar ta kuma bayyana cewa:
“Mutane 138 sun jikkata da raunika iri-iri, 43,936 aka raba su da muhallansu, 8,594 gidaje sun lalace, sannan 8,278 gonaki sun lalace a cikin ƙananan hukumomi 43 da ke cikin jihohi 19.”
An ƙara bayyana cewa yawan mutanen da ambaliyar ta shafa ya haɗa da:
Yara: 53,314
Mata: 36,573
Maza: 24,600
Tsofaffi: 5,304
Nakasa: 1,863
Jihohin da ambaliyar ta shafa sun haɗa da:
Abia, Babban Birnin Tarayya (FCT), Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Borno, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kogi, Kwara, Neja, Ondo, Rivers da Sokoto.
Hukumar NEMA ta bukaci haɗin gwiwar hukumomi da al’ummar da abin ya shafa wajen dakile illolin ambaliya, da kuma kara ɗaukar matakan kariya da rigakafi a nan gaba.



