Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa babban birnin kasar, Abuja, lafiya take kuma an tabbatar da tsaro a cikinta.
Wike ya ce an samu gagarumin ci gaba wajen tsaron Abuja idan aka kwatanta da gwamnatin da ta gabata.
Da yake magana yayin da yake duba aikin gine-gine a yankin Wuye da kuma aikin hanyar tarayya ta 105 daga Umar Musa Yar’Adua Expressway zuwa garin Kuje a ranar Asabar, ministan ya bayyana cewa matsalolin tsaro da ake samun lokaci zuwa lokaci ba su nuna cewa Abuja ba ta da tsaro ba.
Ya ce: “Idan za mu ce akwai gari daya da yafi kowa aminci a wannan kasa, ina ganin Abuja ce. Matsalar da muke da ita ita ce, idan abu daya ya faru, sai mu manta cewa watanni uku baya babu komai da ya faru.
“Ya kamata a yaba mana da jami’an tsaro kan yadda muke aiki tukuru wajen tabbatar da tsaro a Abuja. Abu daya da nake so in jaddada shi ne: Abu daya da ya faru ba yana nufin cewa Abuja ba ta da tsaro ba. Idan akwai gari daya da yafi aminci a wannan kasa, to Abuja ce.”
Ministan ya kuma tabbatar da cewa gwamnati tana daukar matakan tsabtace Abuja ta hanyar cire shara da aka watsar ba bisa ka’ida ba a wurare daban-daban.
Wike ya ce hukumomin FCTA sun fara cire tarkacen shara a kan hanyar filin jirgin sama da kuma a yankin Nyanya/Karshi.
Ya bayyana cewa a cikin makonni biyu masu zuwa za a kammala bayar da sabbin kwangiloli na share shara, inda gwamnati za ta zabi masu kwangila masu cancanta da kwarewa wajen tabbatar da cewa birnin ya kasance cikin tsabta.
Ya ce: “Muna sa ran cewa a cikin makonni biyu, za a kammala bayar da kwangiloli na share shara. Wannan, zan iya tabbatar muku, zai taimaka mana sosai wajen tabbatar da tsabtace birnin.”







