Wani matashi mai suna Stephen Chidubem ya halaka kansa bayan da ya tafka babban hasara a wasan caca da ya kai Naira 500,000, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Lamarin ya faru ne a unguwar Saburi 2 da ke Abuja, a kan titin Abba, a bayan cocin Anglican.
Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da ta’addanci da nazarin tsaro a yankin tafkin Chadi, ne ya bayyana hakan a wata wallafa da ya yi a dandalin X (tsohon Twitter) a ranar Alhamis.
A cewar Makama, Chidubem ya rataye kansa da igiya da ya daure a fan din dakin sa. Bayan samun labarin lamarin, ma’aikatan ceto sun isa wurin da abin ya faru inda suka dauki gawar zuwa Asibitin Gwamnati na Kubwa. Likita ya tabbatar da mutuwar sa, kuma daga nan aka mika gawar zuwa dakin ajiye gawarwaki domin gudanar da binciken gawar (autopsy).
Rahoton ya kara da cewa an samu wata takarda da ya rubuta kafin mutuwar sa, wacce ta nuna cewa dogon shakuwa da wasa caca ne ya jefa shi cikin wannan mummunan hali.
A cikin takardar, Chidubem ya bayyana nadama tare da neman afuwa daga wadanda yake bin bashi da kuma wadanda matsalolin kuɗinsa suka shafa.
“Ina ba kowa hakuri, musamman wadanda suka damu da ni. Amma ba zan iya ci gaba da jefa mutane cikin matsala saboda caca ta ba,” in ji wani bangare na wasiyyar.
Ya kara da cewa: “Don Allah ku yafe mini, Paul, Elvis, da sauran duk abin da nake bin ku. Hakazalika, Bishop Andy Ero, ku bai wa Paul ko Elvis sauran Naira 507,500.”
Bincike ya nuna cewa mamacin yana fama da dogon ciwon jarabar caca wanda ya jefa shi cikin bashi mai yawa da kuma matsin lamba na tunani da damuwa, wanda a karshe ya kai shi ga daukar rayuwarsa da kansa.
