Wasu tsoffin jami’an ƴan sanda sun gudanar da zanga-zanga a bakin ƙofar shiga Majalisar Tarayya da ke Abuja a ranar Litinin, duk da ruwan sama mai tsanani da aka yi.
Tsoffin jami’an sun fito ne domin neman a cire su daga tsarin fansho na Contributory Pension Scheme (CPS), wanda suka bayyana a matsayin tsarin da ke zaluntar su.
Masu zanga-zangar, da yawansu tsofaffi masu shekaru 60 zuwa 70, sun rike kwalaye masu rubuce-rubuce tare da rera wakokin goyon baya, suna zargin gwamnati da watsi da jin daɗin su da mutuncin su bayan sun yi wa ƙasa hidima tsawon shekaru.
Tsohon Babban Jami’in ‘Yan Sanda (CSP), Manir Lawal, ya roƙi gwamnati da ta cire tsoffin ƴan sanda daga tsarin fansho na CPS, yana mai bayyana shi a matsayin wani tsarin da ke cutar da su.
A cewarsa: “Muna nan ne don roƙon gwamnati da ta cire mu daga tsarin CPS. Wannan tsarin zalunci ne kuma rashin adalci ne.”
“Ina da shekara 67. Yawancinmu da kuke gani a nan muna da shekaru 60 zuwa 70. Mun yi wa ƙasa hidima da gaskiya kuma muna da haƙƙin mu yi ritaya da mutunci. Wannan tsarin ya talauta mu. Muna da haƙƙin mu nemi rayuwa mafi kyau,” in ji Lawal.
Tsoffin jami’an sun bayyana cewa ba za su bar wurin ba har sai shugabannin Majalisar sun saurari koke-koken su.
An ga jami’an tsaro a wajen zanga-zangar suna sa ido domin tabbatar da zaman lafiya da kaucewa rikici.



