Ganduje Ya Bayyana Dalilin da Ke Sa ‘Yan Siyasa Sauya Jam’iyya

Abdullahi Umar Ganduje Tsohon Shugaban jam’iyyar APC

Tsohon Shugaban Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce rashin cikakkiyar akida da manufofi a jam’iyyun siyasar Najeriya ne ke haddasa yawaitar sauya sheƙa tsakanin ‘yan siyasa.

Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja yayin ƙaddamar da littafin “Nigeria’s Journey to Democratic Rule”, wanda ɗan jaridar New Telegraph, Onyekachi Eze-Opezulu, ya wallafa.

Tsohon gwamnan Jihar Kano ya ce ya kamata kowace jam’iyya ta kasance da ingantacciyar akida, tsare-tsare da manufofin da suka bambanta ta da sauran jam’iyyu.

A cewarsa, rashin irin wannan ginshiƙi ya raunana tsarin jam’iyyun siyasa a Najeriya, tare da sa ‘yan siyasa ke sauya jam’iyya saboda muradun kansu maimakon bin ƙa’ida ko akida.

Ya ƙara da cewa hakan ya kuma sa ya zama da wahala ga ‘yan Najeriya su fahimci bambancin manufofin jam’iyyun siyasa.

Ganduje ya jaddada buƙatar ƙarfafa dimokuraɗiyya a cikin jam’iyyu da kuma mayar da hankali kan siyasar da ta ginu kan manufofi da batutuwan da suka shafi al’umma, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen bunƙasa dimokuraɗiyya da dawo da amincewar jama’a ga tsarin siyasa.

Ya bayyana cewa dimokuraɗiyya ba ta tsaya ga gudanar da zaɓe kaɗai ba, domin akwai buƙatar mutunta doka, bin kundin tsarin mulki, tabbatar da ingancin hukumomin zaɓe, inganta dimokuraɗiyya cikin jam’iyyu, samar da tsaro, da kuma gudanar da zaɓe cikin ‘yanci da adalci.

Ya ce dole ne a kare waɗannan ginshiƙai domin tabbatar da zaman lafiya na siyasa, haɗin kan ƙasa da ci gaba mai ɗorewa.

Ganduje ya kuma yabawa marubucin littafin, yana mai cewa ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen adana tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya. Ya ce rubuta tarihin sauyin mulkin soja zuwa na farar hula zai amfani masu bincike da kuma al’ummomin da za su zo nan gaba.

Tsohon shugaban na APC ya kuma tuna cewa ya kasance mamba a Jam’iyyar PDP daga shekarar 1998 har zuwa lokacin da ya koma APC a shekarar 2013, yana mai jaddada muhimmancin ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya a ƙasar.

Shi ma da yake jawabi a wajen taron, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Ƙasa, Mohammed Idris, ya bayyana littafin a matsayin muhimmin kundin tarihin tafiyar dimokuraɗiyyar Najeriya, yana mai cewa zai zama wata muhimmiyar madogara ga jama’a, masana da kuma al’ummomin da za su zo nan gaba.

A nasa bangaren, tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Tanko Al-Makura, ya yaba da littafin, yana mai cewa ba wai tarihin siyasa kaɗai yake ɗauke da shi ba, har ila yau jagora ne da ke bayyana gwagwarmaya da nasarorin dimokuraɗiyyar Najeriya.

Al-Makura, wanda ya taba zama sakataren tsohuwar National Republican Convention (NRC) a lokacin Jamhuriya ta Uku, ya buƙaci ‘yan Najeriya su ci gaba da ba da gudunmawa wajen ƙarfafa cibiyoyin dimokuraɗiyya ba tare da la’akari da bambancin siyasa, ƙabila ko addini ba.

Ya ce fahimtar tarihin siyasar Najeriya na da matuƙar muhimmanci wajen kare makomar dimokuraɗiyyar ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *