Central Bank of Nigeria (CBN) ta bayyana cewa tana kara kaimi wajen magance yawan korafe-korafen kwastomomi dangane da kudaden da bankuna ke cirewa da kuma yawan sakonnin sanarwar mu’amala da kwastomomi ke karba daga bankuna.
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ne ya bayyana hakan bayan kammala taron kwamitin manufofin kudi na 305 da aka gudanar a Abuja.
Ya ce batun na samun kulawa daga bangaren masu tsara dokoki a matsayin wani bangare na sauye-sauyen kare hakkin kwastomomi domin inganta gaskiya da amincewa a bangaren harkokin kudi.
Cardoso ya bayyana cewa wasu daga cikin kudaden da kwastomomi ke kokawa a kai, ciki har da cire kudin stamp duty, ba bankuna ne ke anfani da su ba, illa hukumomin gwamnati, yayin da bankunan ajiya ke aiki ne kawai a matsayin masu karba.
Ya kara da cewa CBN na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a bangaren banki ta hanyoyin da aka tsara domin rage rudani da kuma inganta ayyukan bankuna ga kwastomomi.
A cewarsa, daya daga cikin manyan matsalolin da ake dubawa shi ne yawaitar sakonnin sanarwar mu’amala da ake aikawa kwastomomi, wanda kan haddasa rashin fahimta da zargin maimaita caji.
Ya ce CBN na aiki tare da bankuna domin inganta tsarin sadarwa tare da duba yiwuwar hada sakonnin sanarwar mu’amala wuri guda, domin kwastomomi su fahimci cire kudade da cajin da aka yi musu ba tare da rudani ba.
Baya ga korafe-korafen kwastomomi, CBN ta kuma yi amfani da taron kwamitin manufofin kudi wajen bayyana ci gaban da aka samu a bangaren tattalin arziki, musamman karin rancen da ake bai wa kananan da matsakaitan masana’antu.
Cardoso ya ce sabbin bayanai sun nuna cewa bankuna na kara mayar da hankali wajen bayar da rance ga kananan da matsakaitan sana’o’i yayin da suke sake nazarin hadarin bashi da damar bunkasa kasuwanci.
Ya bayyana cewa kananan da matsakaitan sana’o’i suna da muhimmanci wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya, yana mai cewa samar musu da damar samun rance na daga cikin manyan abubuwan da gwamnati da hukumomi ke bai wa fifiko.
Ya kuma bayyana cewa CBN na tallafa wa wannan sauyi ta hanyar gyare-gyaren dokoki da hukumomi, ciki har da hadin gwiwa da Nigerian Communications Commission (NCC) domin rage matsalolin aiki da ke shafar harkokin hada-hadar kudi ta zamani da gudanar da kananan sana’o’i.
A cewarsa, shirye-shirye irin su tsarin Global Standing Instruction (GSI) da gyare-gyaren cibiyoyin bayar da tallafin kudi suna da nufin inganta hanyoyin dawo da bashi da kuma fadada damar samun kudaden jari ga kananan kasuwanci.
Cardoso ya jaddada cewa CBN tana kallon kanta a matsayin mai samar da yanayi mai kyau maimakon mai bayar da rance kai tsaye, ta hanyar amfani da manufofi da hadin kai wajen karfafa bankunan kasuwanci su kara bayar da rance ga bangarorin da ke samar da ci gaban tattalin arziki, musamman kananan da matsakaitan sana’o’i.
Ya kara da cewa duk da akwai kalubale, alamun farko sun nuna cewa bankuna na kara nuna sha’awar bayar da sababbin rance ga kananan sana’o’i, wanda ke nuna sauyin dabarun bayar da bashi a tsarin harkokin kudi na kasar.
CBN ta sake jaddada kudirinta na karfafa kariyar kwastomomi, inganta gaskiya a ayyukan bankuna, da kuma tallafa wa bunkasar bayar da rance ga kowa a matsayin wani bangare na sauye-sauyen bangaren harkokin kudi.

