Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke jadawalin zaben shekarar 2027 da Independent National Electoral Commission (INEC) ta fitar.
Mai shari’a Mohammed Umar, a hukuncin da ya yanke kan karar da jam’iyyar Youth Party ta shigar, ya ce matakin da INEC ta dauka ya kakaba wa jam’iyyun siyasa takaitattun lokuta wajen gudanar da zabukan fidda gwani da sauran harkokin kafin zabe, wanda ya saba wa tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2026.
Mai shari’ar ya bayyana cewa INEC ba ta da ikon doka na sanya ko kayyade lokacin da jam’iyyun siyasa za su gudanar da zabukan fidda gwani domin tsayar da ‘yan takara a babban zaben 2027.
Jam’iyyar Youth Party ce ta shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CS/517/2026 inda ta maka INEC a matsayin wacce ake kara ita kadai.
A cikin karar da aka shigar ranar 11 ga watan Maris, jam’iyyar ta bukaci kotu ta yi mata tanadi guda shida, kuma kotun ta amince da dukkan bukatun nata.
Mai shari’a Umar ya bayyana cewa INEC ba za ta iya rage ko takaita wa’adin da Dokar Zabe ta tanada ba dangane da mika bayanan ‘yan takara, janye ko maye gurbin ‘yan takara da sauran batutuwa makamantan haka.
Saboda haka, kotun ta soke sassan jadawalin zabe da tsarin ayyukan babban zaben 2027 da INEC ta sake fitarwa, wadanda suka sanya lokutan da suka saba wa Dokar Zabe ta 2026.
Kotun ta bayyana cewa ikon da Dokar Zabe ta bai wa INEC na karbar sanarwar zabukan fidda gwani da bayanan ‘yan takara, da kuma lura da zabukan, bai hada da ikon kayyade lokacin da jam’iyyun siyasa za su gudanar da zabukan fidda gwani ba.
Haka kuma kotun ta ce bisa tanadin Sashe na 29(1) na Dokar Zabe ta 2026, wanda ya bai wa jam’iyyun siyasa damar mika bayanan ‘yan takara har zuwa kwanaki 120 kafin zabe, INEC ba za ta iya rage wannan wa’adi ta hanyar sanya gajeren lokaci a jadawalinta ba.
Kotun ta kuma ce bisa Sashe na 31 na dokar, jam’iyyu na da damar janye ko maye gurbin ‘yan takara har zuwa kwanaki 90 kafin zabe, saboda haka INEC ba za ta iya sanya wa’adin da ya fi haka gajarta ba.
Haka zalika, kotun ta bayyana cewa INEC ba ta da ikon fitar da cikakken jerin ‘yan takara kafin cikar mafi karancin kwanaki 60 da doka ta tanada.
Mai shari’ar ya kara da cewa INEC ba ta da ikon sanya a jadawalinta cewa yakin neman zabe zai kare kwanaki biyu kacal kafin gudanar da zabe.
Kotun ta kuma bayyana cewa wa’adin da INEC ta sanya na mika rajistar mambobin jam’iyya ba zai shafi zabukan fidda gwani da ake gudanarwa domin maye gurbin ‘yan takarar da suka janye ba.
Daga karshe, kotun ta soke duk wasu wa’adoyi da INEC ta sanya a jadawalin zaben 2027 da suka shafi gudanar da zabukan fidda gwani, tana mai cewa sun saba wa tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2026.

