Gwamna Fubara ya Janye Daga Takarar Gwamnan Rivers

Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanar da janyewarsa daga zaben fidda gwani na gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Fubara ya ce ya dauki wannan mataki ne bayan tuntubar iyali, abokai da kuma abokan siyasarsa, yana mai jaddada cewa muradin kai bai kamata ya fi maslahar al’ummar Jihar Rivers muhimmanci ba.

Dan takarar ya gode wa magoya bayansa bisa goyon baya da sadaukarwar da suka nuna a tafiyarsa ta siyasa, tare da amincewa cewa janyewar na iya bata wa mutane da dama rai.

Ya bayyana cewa bukatar zaman lafiya, hadin kai da kwanciyar hankali a jihar ne ya sanya ya dauki wannan mataki, yana mai cewa shirun da ya yi a makonnin baya ya kasance ne domin kare muradun jihar.

Yayin da ya yi ishara da wasu sabbin sauye-sauyen siyasa, gwamnan ya ce akwai wasu batutuwa da ya dace a warware su cikin lumana domin tabbatar da zaman lafiya, yana mai jaddada cewa matakin da ya dauka ba saboda tsoro ko rauni ba ne.

Fubara ya kuma yabawa shugabannin APC da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa goyon baya da karfafa gwiwar da suka ba shi.

Sannan ya bukaci mambobin jam’iyyar da su ci gaba da kasancewa cikin hadin kai tare da jajircewa wajen marawa jam’iyyar baya gabanzaɓenben gwamna mai zuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *