Trends

Masu Sayar da Man Fetur Sun Yi Fatali da Karar Dangote Kan Shigo da Fetur

Sabuwar takaddama ta barke a bangaren kasuwancin mai a Najeriya, inda dillalan mai da masu ajiye fetur suka yi watsi da karar da matatar Dangote Petroleum Refinery ta shigar kotu kan batun hana shigo da fetur daga kasashen waje.

Matatar ta garzaya Babbar Kotun Tarayya da ke Legas tana neman a soke lasisin shigo da fetur da Hukumar Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority ta bai wa wasu kamfanoni kwanan nan.

Dangote ya yi hujja da cewa lasisin ya sabawa dokar Petroleum Industry Act, wadda ke ba da damar shigo da mai ne kawai idan akwai karancin wadata a cikin gida.

NMDPRA ta bai wa kamfanoni shida lasisin shigo da fetur, wadanda suka hada da NIPCO, AA Rano, Matrix Energy, Shafa, Pinnacle Oil da Bono Energy, domin shigo da kusan tan 720,000 na fetur. Hukumomi sun ce matakin ya zama dole domin tabbatar da wadatar mai a kasuwa da hana karancin kaya.

Sai dai Dangote Petroleum Refinery ta ce matatar ta na da karfin samar da gangar mai 661,000 a rana, kuma tana shirin kara karfin zuwa ganga miliyan 1.4 a rana cikin watanni 30 masu zuwa, tare da amfani da danyen mai daga Najeriya da kasashen waje.

Kungiyar masu ajiye mai da dillalan man fetur ta Najeriya (DAPPMAN) ta yi kakkausar suka ga karar, tana gargadin cewa hakan na iya dagula kasuwar mai a kasar.

Ta ce, “Lasisin shigo da mai da ake magana a kai ba wata rangwame ba ce kawai. Su kayan doka ne da ke tabbatar da dorewar samar da mai, ba wai don cutar da wani kamfani guda ba.”

Haka kuma, Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Kasa (IPMAN) ta bayyana adawa da matakin, tana mai cewa idan matatar Dangote ta rage farashi zuwa matakin da ya dace, shigo da mai zai ragu da kansa.

Mataimakin Shugaban IPMAN, Hammed Fashola, ya ce matakin na iya haifar da fargabar mamaye kasuwa daga kamfani daya kadai.

Kungiyar Masu Gidajen Sayar da Man Fetur ta Najeriya (PETROAN) ita ma ta ce shigo da mai doka ce a karkashin tsarin cire tallafin mai, don haka karar ba ta da bukatar a kotu.

Shugaban kungiyar, Billy Gillis-Harry, ya ce har yanzu ‘yan kasuwa na fuskantar jinkiri wajen karbar kayayyaki duk da sun biya, lamarin da ke nuna cewa har yanzu ba a kai matakin wadatar da kasuwa ba.

A gefe guda kuma, Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya kare tallafin gwamnati ga Dangote Petroleum Refinery yayin wani taro a Kigali, inda ya ambaci yarjejeniyar sayen danyen mai da naira da kuma sassaucin lasisi.

Ya ce, “A cikin matsalar da duniya ke ciki, Najeriya mai mutane sama da miliyan 200 ba za ta iya rayuwa cikin kwanciyar hankali ba tare da matatar mai ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *