Kwararrun likitoci sun yi gargadin cewa cutar hawan jini na kara yaduwa cikin sauri a tsakanin ‘yan Najeriya masu kasa da shekara 40, sakamakon rayuwar rashin lafiya, rashin zuwa duba lafiya da kuma tarihin cutar a iyali.
Da take jawabi yayin bikin Ranar Hawan Jini ta Duniya ta shekarar 2026, Temilade Adeyanju ta bayyana cewa mafi yawan masu fama da cutar ba sa sanin suna dauke da ita har sai sun fara samun matsaloli masu tsanani.
Ta ce, “A mafi yawan lokuta, masu fama da cutar ba sa sanin suna da hawan jini, hakan na sa su je asibiti ne bayan sun fara fuskantar matsalolin da za a iya kauce musu.”
Adeyanju ta bayyana cewa ma’aunin gano hawan jini ya bambanta a kasashe da kungiyoyi daban-daban. Ta ce kungiyar masu kula da zuciya ta Najeriya da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suna daukar ma’aunin 140/90mmHg a matsayin hawan jini, yayin da American Heart Association da Hukumar CDC ta Amurka ke daukar duk wanda ya haura 130/80mmHg a matsayin mai hawan jini.
Ta shawarci ‘yan Najeriya da su tabbatar hawan jininsu bai wuce 120/80mmHg ba domin kauce wa hadari.
An bayyana hawan jini a matsayin “mai kashe mutane cikin shiru” saboda yana tasowa ba tare da wata alama ba, amma yana iya haddasa bugun jini, ciwon zuciya, lalacewar koda, matsalolin jima’i da makanta.
A cewarta, mutane takwas cikin goma da ba a gano suna da hawan jini ba kan isa dakin gaggawa ne bayan sun fara fama da matsaloli masu tsanani.
Ta lissafa abubuwan da ke kara haddasa cutar da suka hada da ciwon sukari, kiba, yawan kitse a jini, rashin kula da hawan jini da kuma wasu cututtuka masu alaka da kumburi a jiki. Haka kuma ta ce rashin cin abinci mai kyau, shan giya, taba sigari da damuwa suna daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa cutar.
Shi ma Ifeoluwa Odedina ya bayyana cewa mutane da dama na rayuwa da hawan jini ba tare da sun sani ba.
Ya yi nuni da wani bincike da aka gudanar a Ibadan a shekarar 2025 wanda ya nuna cewa kashi 10.2 cikin 100 na mutane na dauke da hawan jini ba tare da an gano ba.
A cewarsa, “Ya kamata duk wani baligi ya rika duba hawan jininsa akalla sau biyu a shekara.”
Odedina ya ce yawan amfani da gishiri, damuwa da shan giya suna daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa hawan jini, musamman a tsakanin bakar fata. Ya kara da cewa shiga tsarin inshorar lafiya na taimakawa wajen samun magani da kuma bin umarnin likitoci yadda ya kamata.
Kwararrun biyu sun yi kira da a kara wayar da kan jama’a, a rika gudanar da gwaje-gwajen gano cutar akai-akai, tare da samar da manufofin gwamnati da za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar da kuma kula da masu fama da ita.
A karshe, Temilade Adeyanju ta bukaci jama’a da su hada kai wajen yaki da cutar, tana mai cewa dole ne a kara wayar da kai domin rage illar “mai kashe mutane cikin shiru” a cikin iyalai da al’umma baki daya.
