Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa Najeriya na kan hanyar jawo kusan dala biliyan 20 na jarin waje kai tsaye (FDI) a shekarar 2026 kaɗai.
Tinubu ya danganta hakan da cire matsalolin da suka daɗe suna hana zuba jari, daidaita tattalin arziki da kuma gyare-gyaren da gwamnatinsa ta yi domin ƙara gaskiya da sauƙaƙa harkokin kasuwanci.
Shugaban ya bayyana haka ne yayin taron Africa CEO Forum da aka gudanar a birnin Kigali na ƙasar Rwanda, inda ya yi kira ga ƙasashen Afirka su dogara da kansu tare da haɗa albarkatun nahiyar domin bunƙasa tattalin arziki.
A yayin wata tattaunawa da fitacciyar ’yar jaridar Birtaniya, Zainab Badawi, ta jagoranta tare da shugaban ƙasar Gabon, Brice Clotaire Oligui Nguema, Tinubu ya ce dole ne Afirka ta daina fitar da albarkatun ƙasa a ɗanye tana sake shigo da su bayan an sarrafa su a farashi mai tsada.
Ya ce cire cikas da matsalolin da ke hana kasuwanci zai ƙara ƙarfafa masu zuba jari daga ƙasashen waje su kawo jarinsu Najeriya.
Tinubu ya ce, “A bana kaɗai zan iya bugun ƙirji cewa Najeriya na jan kusan dala biliyan 20 na jarin waje kai tsaye.”
Da yake magana kan ƙarin darajar albarkatun ƙasa, shugaban ya bayyana cewa zamanin fitar da albarkatun Najeriya ba tare da an sarrafa su ba ya ƙare.
Ya ce, “Ba wanda zai ɗauki ƙarafa daga Najeriya ba tare da an ƙara musu daraja ba. Zan iya samar da batirin motoci daga ma’adanan ƙasata.”
Shugaban ya kuma ce ya kamata Afirka ta yi amfani da albarkatunta wajen samar da kuɗaɗen bunƙasa tattalin arzikinta maimakon dogaro da wasu ƙasashe.
Game da Dangote Petroleum Refinery, wadda ke tace ganga 650,000 na mai a kullum kuma ke samar da kusan kashi 70 cikin ɗari na buƙatar man fetur ta Najeriya, Tinubu ya ce haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu ne ya sa hakan ya yiwu.
Ya ce, “Najeriya ba za ta iya rayuwa cikin kwanciyar hankali da mutane sama da miliyan 200 ba tare da matatar mai ba. Dole gwamnati ta ƙarfafa masu ɗaukar haɗari irin su Aliko Dangote.”
Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta tallafa wa Dangote ta hanyar ba shi damar kasuwanci cikin sauƙi, lasisi da kuma samar masa da ɗanyen man da yake buƙata.
Ya ce yanzu matatar Dangote na fitar da fetur, man jiragen sama da sauran kayayyakin mai zuwa ƙasashen waje.
Da yake magana kan sayar da ɗanyen mai ga matatar cikin kuɗin naira, Tinubu ya ce, “Idan kuɗin ƙasar Najeriya naira ne, me zai hana a sayar wa matatar cikin naira? Hakan yana rage wahalar canjin kuɗi da matsalar hauhawar farashin dala.”
Shugaban ya kuma soki hukumomin ƙididdigar tattalin arziki na ƙasashen yamma, yana mai cewa suna raina ƙarfin tattalin arzikin ƙasashen Afirka duk da irin ci gaban da suke samu.
A bangaren haraji, Tinubu ya ce an yi gyaran tsarin haraji domin ya zama mai sauƙin fahimta ga kowa, yana mai cewa yanzu ana iya biyan haraji ta wayar hannu cikin sauƙi.
Ya ce tsarin da aka fara a jihar Lagos State ya taimaka wajen mayar da Lagos ɗaya daga cikin manyan tattalin arziki a Afirka, kuma ana aiwatar da irin wannan tsarin a matakin ƙasa baki ɗaya.
Kan noma kuwa, shugaban ya ce gwamnati ta samar da yankuna 6,000 na noma mai amfani da injuna tare da shirye-shiryen sayen amfanin gona daga manoma domin kare su daga faɗuwar farashi.
Ya kuma ambaci aikin titin Sokoto zuwa Badagry mai tsawon kilomita 1,000 a matsayin wani babban aikin da zai taimaka wajen sufuri da kasuwanci a yankin Yammacin Afirka.
A bangaren fasahar sadarwa, Tinubu ya bayyana cewa an shimfiɗa sama da kilomita 90,000 na igiyoyin fibre optic a faɗin Najeriya domin bunƙasa sadarwa, ilimi da kasuwancin zamani.
Ya ce Afirka dole ta rungumi fasahar zamani kamar basirar wucin gadi (AI) da kasuwancin intanet domin ta yi gogayya da sauran duniya.
Da yake magana kan matasan Najeriya, shugaban ya ce dole gwamnati ta shirya su domin juyin juya halin fasahar zamani, yana mai cewa idan ba haka ba, za su iya ƙin zaɓensa a gaba.
Tinubu ya kuma yi kira da a aiwatar da yarjejeniyar kasuwancin bai ɗaya ta Afirka yadda ya kamata domin ƙasashen nahiyar su yi aiki tare wajen cin gajiyar albarkatunsu.
Taron Africa CEO Forum na Kigali shi ne mafi girman taron shugabannin kamfanoni da shugabannin ƙasashen Afirka, inda ake tattauna hanyoyin bunƙasa tattalin arziki da haɗin kan kasuwanci a nahiyar.
