Nigerian National Petroleum Company Limited (NNPC Ltd.) ta bayyana cewa sabon yarjejeniyar fahimtar juna da ta kulla da wasu kamfanonin ƙasar China guda biyu ba sabuwar yarjejeniyar kashe kuɗi ba ce ko bayar da kwangila.
An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne da Sanjiang Chemical Company Limited da Xingcheng Industrial Park domin nazarin yiwuwar haɗin gwiwa wajen kammala da kuma gudanar da matatun mai na Port Harcourt da Warri.
Wani babban jami’in NNPC ya ce yarjejeniyar ba ta ƙunshi bayar da kuɗi kai tsaye ba, illa dai fahimtar juna tsakanin ɓangarorin da ke son binciken hanyoyin gyarawa da faɗaɗa ƙarfin matatun man.
Ya bayyana cewa yarjejeniyar ta haɗa da yiwuwar haɗin gwiwa a fannoni kamar tsarin samar da kuɗi, gudanarwa da kula da matatun, haɗa harkokin sinadarai da kuma ayyukan masana’antu masu amfani da iskar gas, ba tare da amfani da kuɗin gwamnati ba.
Jami’in ya jaddada cewa tun daga shekarar 2025 NNPC ba ta amince ko kashe wani sabon kuɗi wajen gyaran matatun mai ba, yana mai cewa yanzu kamfanin na aiki ne ƙarƙashin dokar Petroleum Industry Act a matsayin kamfani mai cin gashin kansa.
A cewarsa, “ba a kashe ko sisi wajen gyaran matatun ba, kuma babu shirin cire kuɗi kai tsaye daga asusun kamfanin.”
Babban Daraktan NNPC, Bashir Bayo Ojulari, ya ce matsalolin tace mai a Najeriya ba matsalar kuɗi kaɗai ba ce, har ma tana da alaƙa da fasaha da ƙwarewa, wanda ke bukatar gogaggun abokan hulɗa.
Ya ce sabon tsarin haɗin gwiwar hannun jari zai tabbatar da gaskiya da ɗaukar alhaki, domin abokan hulɗar za su samu riba ne kawai idan matatun mai sun yi aiki yadda ya kamata.
Ojulari ya ƙara da cewa matatun mai na zamani dole su zama cibiyoyin makamashi da ke haɗa tace mai, sinadarai, takin zamani da kuma sarrafa iskar gas domin samar da fa’ida ga tattalin arziki.
Yarjejeniyar na nuna sauyin da NNPC ke yi daga tsarin gyaran matatun da gwamnati ke ɗaukar nauyi zuwa tsarin haɗin gwiwa mai anfani ga kasuwanci, domin dawo da matatun mai cikin aiki mai ɗorewa bayan shekaru na kashe kuɗi ba tare da samun sakamako mai gamsarwa ba.
