Trends

Ƙarancin Man Jiragen Sama Na Barazana Ga Tsaron Tashi da Sauka – Matuka Jirgi

National Association of Aircraft Pilots and Engineers (NAAPE) ta nuna damuwa kan ci gaba da ƙarancin man jiragen sama na Jet A1, tana mai gargaɗin cewa matsalar na fara barazana ga tsaron sufurin jiragen sama, ayyukan kamfanonin jiragen sama da walwalar ma’aikata.

Shugaban NAAPE, Bunmi Gindeh, ya bayyana matsalar ƙarancin man Jet A1 a matsayin abin damuwa na ƙasa wanda ke bukatar gaggawar shiga tsakani daga hukumomin kula da harkokin jiragen sama da makamashi.

Ya ce matsalar ta haifar da jinkirin tashin jirage, sauya hanyoyin zirga-zirga da kuma tsawaita lokutan aikin ma’aikatan jirgi, lamarin da ka iya rage matakan tsaro a harkar sufurin jiragen sama.

A cewarsa, “gajiya na rage ƙwaƙwalwar tunani, tana jinkirta saurin daukar mataki, kuma mafi hatsari, tana rage fahimtar yanayin da ake ciki.”

Matsalar na zuwa ne a lokacin da kamfanonin jiragen sama na cikin gida ke fama da tsadar gudanar da aiki da tashin gwauron zabi na farashin mai, lamarin da ke sauya tsarin tattalin arzikin harkar jiragen sama a Najeriya.

NAAPE ta yi gargaɗin cewa jiragen da suka tsaya ko suka yi jinkiri ba sa samar da kuɗaɗen shiga, yayin da kuɗaɗen gudanarwa ke ci gaba da taruwa, abin da ke ƙara jefa kamfanonin jiragen sama cikin matsin tattalin arziki tare da shafar ma’aikata ta hanyar jinkirin albashi da ƙarancin walwala.

Ƙungiyar ta ce idan matsalar ta ci gaba, wasu kamfanonin jiragen sama na iya dakatar da wasu hanyoyin zirga-zirga ko ma rufe baki ɗaya, wanda hakan zai haddasa asarar ayyukan yi da rage haɗin kai a harkokin sufuri a faɗin ƙasar.

NAAPE ta ambaci rage wasu hanyoyin zirga-zirga da Rano Air ta yi a baya-bayan nan a matsayin wata alama ta matsin lambar da kamfanonin jiragen sama ke fuskanta.

Ƙungiyar ta buƙaci Gwamnatin Tarayya, Nigerian Civil Aviation Authority (NCAA), Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA), da masu samar da mai su ɗauki magance matsalar Jet A1 a matsayin gaggawar ƙasa domin kare tsaron jiragen sama da daidaiton harkar sufurin jiragen sama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *