Gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da wani shiri na Yuro miliyan 4.2 da European Union (EU) ke tallafawa tare da aiwatarwa daga World Health Organization (WHO), domin ƙarfafa damar ƙasar wajen gano barkewar cututtuka da kuma mayar da martani cikin gaggawa.
Shirin mai suna EU Support to Public Health Institutes in Nigeria (EU SPIN) zai gudana na tsawon shekaru huɗu tare da haɗin gwiwar Federal Ministry of Health and Social Welfare.
An tsara shirin ne domin inganta haɗin kai tsakanin cibiyoyin kula da lafiyar jama’a, musayar bayanai, da kuma ƙarfafa ƙwarewar ma’aikata a fannin lafiya.
Karamin Ministan Lafiya na Najeriya, Iziaq Adekunle Salako, ya bayyana shirin a matsayin “wani babban mataki” wajen ƙarfafa tsarin kiwon lafiyar Najeriya.
Ya ce, “Shirin zai taimaka wajen inganta rayuwar ‘yan Najeriya, musamman masu rauni da ke bukatar kulawa ta musamman.”
Najeriya na ci gaba da fama da barkewar cututtuka kamar kwalara, diphtheria, zazzabin Lassa, sankarau da Mpox, baya ga ƙaruwa da cututtukan da ba sa yaɗuwa kamar hawan jini da ciwon sukari.
Bayanan World Health Organization sun nuna cewa cututtukan da ba sa yaɗuwa suna haddasa kashi 27 cikin 100 na mace-mace a Najeriya, yayin da cutar zazzabin cizon sauro ke haddasa kusan kashi 30 cikin 100 na mace-macen malaria a duniya.
Shirin EU SPIN zai magance gibin da ke cikin tsarin kula da lafiya ta hanyar fayyace rawar da hukumomin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi za su taka, tare da samar da tsarin bayanai na lokaci-lokaci domin yanke shawara cikin sauri yayin matsalolin lafiya.
Wani muhimmin ɓangare na shirin shi ne horas da ma’aikatan lafiya, inda ake sa ran horar da kusan kashi 75 cikin 100 na ma’aikatan lafiyar jama’a kan jagoranci, kariya daga cututtuka, hanyoyin mayar da martani da kuma fasahar dijital.
Jakadan European Union a Najeriya, Gautier Mignon, ya ce shirin na nuna haɗin kai wajen gina ingantaccen tsarin lafiya mai ɗorewa.
A cewarsa, “Ta hanyar EU SPIN, Tarayyar Turai na zuba jari wajen gina cibiyoyin kula da lafiyar jama’a masu ƙarfi tare da amfani da fasahar zamani a Najeriya.”
Shi ma wakilin World Health Organization a Najeriya, Pavel Ursu, ya ce inganta haɗin kai, ƙwarewa da kayan aikin dijital zai taimaka wajen kare rayuka da kuma tabbatar da lafiyar al’umma.
Ana sa ran zuwa shekarar 2028 shirin zai samar da ingantacciyar haɗin kai tsakanin hukumomi, fayyace nauyin da kowace hukuma ke da shi, da kuma ƙarfafa tsarin bayanan lafiyar jama’a a faɗin ƙasar ta hanyar tsarin sa ido da bita lokaci zuwa lokaci.
