Tsohon ɗan majalisar wakilai daga Jihar Gombe, Khamisu Ahmed Mailantarki, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Mailantarki, wanda ya kasance ɗan takarar gwamna na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a zaɓen 2023, ya miƙa takardar bayyana aniyarsa a sakatariyar PDP ta jiha da ke Gombe a ranar Litinin.
Daraktan kamfen ɗinsa, Malam Adamu Bappah, ya bayyana Mailantarki a matsayin jagora mai kusanci da talakawa, wanda ke shirye koyaushe ya yi aiki domin al’umma da cigaban Jihar Gombe baki ɗaya.
A cewarsa, burin Mailantarki na zama gwamna ya ƙarfafa gwiwar ‘yan siyasa da dama, inda ya iso tare da kusan ‘yan takarar majalisar dokokin jiha guda 20 da magoya baya masu neman mukamai daban-daban a ƙarƙashin PDP.
Ya ƙara da cewa Mailantarki ya nuna ƙwarewa a jagoranci, kasancewar ya wakilci mazabun Gombe/Kwami/Funakaye a majalisar wakilai tsakanin shekarun 2011 zuwa 2015, inda ya ba da kyakkyawan wakilci.
A cikin takardar da ya miƙa wa shugabannin jam’iyyar, Mailantarki ya ce burinsa ya samo asali ne daga nauyin da yake ji da kuma ƙudurin yi wa jama’a hidima.
Ya ce: “Ina da tabbacin cewa da haɗin kan shugabancin jam’iyyarmu da masu ruwa da tsaki, za mu ƙara ƙarfafa dimokuraɗiyya tare da bunƙasa tattalin arzikin Jihar Gombe domin amfanin kowa.
“Don haka ina neman goyon baya, shawarwari da haɗin kai daga shugabannin jam’iyya a kowane mataki yayin da nake gabatar da kaina domin wannan muhimmin nauyi.”
Da yake karɓar takardar a madadin jam’iyyar, mataimakin shugaban PDP na jiha, Adamu Dan’Azumi, ya ce bayyana aniyar Mailantarki na nuna yadda amincewa da jam’iyyar ke ƙaruwa gabanin zaɓen 2027.
Ya ce yawaitar masu neman takara a jam’iyyar na nuna cewa jam’iyyun adawa na ƙara samun ƙarfi a jihar.
Dan’Azumi ya yabawa Mailantarki bisa gabatar da takardarsa da wuri, tare da tabbatar da cewa za a gudanar da zaɓen fidda gwani cikin gaskiya da adalci.
Ya kuma sanar da cewa PDP ta tsawaita wa’adin karɓar fom na nuna sha’awa daga ranar 3 ga Mayu zuwa 9 ga Mayu, tare da kira ga duk masu sha’awar takara su yi amfani da wannan dama.
Tun da farko, Sakataren PDP na jiha, Adamu Haruna Abubakar, ya buƙaci masu ruwa da tsaki a ƙananan hukumomi su ƙara jajircewa wajen jawo hankalin masu neman takara su karɓi tare da miƙa fom.
Ya ce: “PDP za ta fitar da ɗan takara. Bai kamata mu yanke ƙauna ba. Kowa ya fito ya tsaya tsayin daka, ya tattara jama’a, kuma mu fafata a wannan zaɓe da gaske.”









