Bayan makonni ana ta hasashe kan makomarsu ta siyasa sakamakon rikicin da ke addabar jam’iyyar ADC, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, da takwaransa na jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, sun sanar da komawarsu jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a hukumance.
Manyan ‘yan siyasar biyu sun bayyana wannan mataki ne yayin wata ziyara da suka kai gidan jagoran NDC na ƙasa, Seriake Dickson, inda suka gana da manyan jiga-jigan jam’iyyar.
Rahotanni sun nuna cewa Obi da Kwankwaso sun isa wajen da misalin ƙarfe 5:14 na yamma, inda suka shiga tattaunawa ta sirri da Dickson da sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar, lamarin da ke nuna sabon babi a tafiyarsu ta siyasa.
Taron ya gudana ne a bayan ƙofofi rufe kuma ya ƙare da misalin ƙarfe 6:45 na yamma. Da yake magana bayan kammala taron, Kwankwaso ya yi kira ga magoya bayansa da abokan siyasa da su mara wa NDC baya, yana mai ƙarfafa su su shiga jam’iyyar da ƙarfi.
A nasa bangaren, Obi ya shawarci ‘yan jam’iyyar da su guji garzayawa kotu kan rikice-rikice, yana mai jaddada muhimmancin warware matsaloli a cikin gida.
Ana kallon wannan sauyi a matsayin babban ci gaba ga NDC, ganin cewa duka ‘yan siyasar biyu na da dimbin magoya baya a sassa daban-daban na ƙasar nan.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a daren Asabar, Kwankwaso ya bayyana cewa rikicin da ya sa shi da mabiyansa suka fice daga NNPP yanzu ya fara shafar ADC.
Ya ce sakamakon hakan, yana ci gaba da tuntuba da bangarori daban-daban, inda ya amince cewa ana tattaunawa da jam’iyyun NDC da PRP kafin daga bisani ya yanke shawarar komawa NDC.
Kwankwaso ya kuma fayyace batun takarar shugaban ƙasa a ADC, yana mai cewa bai yanke hukuncin neman tikitin jam’iyyar ba.
Shi ma Peter Obi ya bayyana cewa barin da ya yi wa ADC ba saboda wani rashin kyautatawa daga shugabannin jam’iyyar ba ne.
Ya ce: “Ba don shugabanmu mai girma, Sanata David Mark, ya yi min wani abu ba, haka kuma ba don jagorana kuma babban ɗan’uwa na, Alhaji Atiku Abubakar, ko wani daga cikin shugabannin jam’iyyar ya yi min laifi ba. Zan ci gaba da girmama su.
“Amma tsarin siyasar Najeriya da hukumominsa da suka haddasa rikice-rikicen da suka tilasta min barin Labour Party, yanzu suna neman shiga cikin ADC, tare da yawaitar shari’o’i, rikice-rikice na cikin gida, zargi da rarrabuwar kai, maimakon mayar da hankali kan manyan matsalolin ƙasa da kuma siyasar hidima da gina ƙasa.”







