Kasashe uku na Yammacin Afirka — Benin, Togo da Nijar — Najeriya na bin bashin kimanin dala miliyan 9.55 kan wutar lantarki da aka samar musu a rubu’i na karshe na shekarar 2025, a cewar Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC).
Rahoton NERC na rubu’i na hudu (Q4) na shekarar 2025 ya nuna cewa mai kula da kasuwar wutar lantarki ya fitar da takardun biyan kudi na dala miliyan 20.44 ga kasashen uku, amma an samu biyan dala miliyan 10.89 kacal, wanda ke nuna kashi 53.28 cikin 100 na biyan kudin.
Rahoton ya bayyana cewa, “Wannan na nufin daga kowanne dala 100 da aka caje, an biya dala 53.28 ne kawai, inda aka bar gibin dala 46.72.”
Rarrabuwar biyan kudin ya nuna bambancin yadda kasashen suka biya: Paras-SBEE (Benin) ta biya kashi 68.16, Paras-CEET (Togo) ta biya kashi 64.97, yayin da Transcorp-SBEE (Ughelli) ta biya kashi 12.30 kacal.
Sai dai Transcorp-SBEE (Afam 3) ta yi kokari da biyan kashi 82.31, yayin da Mainstream-NIGELEC (Nijar) ta biya kashi 68.63. Amma Odukpani-CEET (Togo) ba ta biya ko sisin kwabo ba.
Hukumar NERC ta kara da cewa kamfanin wutar lantarki na Benin, SBEE, ya sake biyan karin dala miliyan 3.54 domin rage bashin da yake kansa, yayin da wani mai amfani da wuta a cikin gida a Najeriya, APLE, ya biya Naira miliyan 141 na tsohon bashi.
A gefe guda kuma, masu sayen wuta a cikin gida na Najeriya sun nuna kyakkyawan hali wajen biyan kudi, inda suka biya Naira biliyan 3.5 daga cikin Naira biliyan 4.17 da aka caje su, wanda ke nuna kashi 84.23 cikin 100 na biyan kudin.
Sai dai kamfanin Ajaokuta Steel, wanda aka sanya shi a matsayin mai amfani na musamman, an caje shi Naira biliyan 1.26 amma bai biya komai ba a lokacin.
Rahoton ya nuna cewa Najeriya na fuskantar matsaloli wajen karbar kudin wutar lantarki da take sayarwa zuwa kasashen waje, duk da cewa kasar na fama da karancin wutar lantarki a cikin gida. Wannan bashin dala miliyan 9.55 na kara jaddada matsin tattalin arziki da ke kan kamfanonin samar da wutar lantarki a Najeriya.
