Hukumar Inshorar Ajiya ta Najeriya (NDIC) ta fara matakin karshe na rufe bankuna 89 na kananan kudi (microfinance) da na gidaje (mortgage) da suka gaza, bayan da sabbin masu zuba jari suka karbe su.
A cikin wata sanarwa da Shugabar Sadarwa ta NDIC, Hawwau Gambo, ta sanya wa hannu, hukumar ta ce wannan mataki na daga cikin kokarin kammala rufe wadannan bankuna da suka daina aiki bayan an warware matsalolinsu ta hanyar tsarin “Purchase and Assumption (P&A)”.
Bankunan da abin ya shafa suna cikin bankuna 179 na microfinance da kuma bankuna hudu na mortgage da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya soke lasisinsu a watan Mayu na shekarar 2023.
A karkashin wannan tsari, sabbin masu zuba jari sun karbi kadarori da basussukan bankunan, sannan suka ci gaba da gudanar da ayyukansu karkashin sabbin sunaye.
Sanarwar ta ce, “NDIC, a matsayinta na mai kula da rufe bankunan, za ta gabatar da bukatun kotu a sassa daban-daban na Kotun Tarayya domin samun umarnin kammala rushe bankunan da kuma sakin hukumar daga wannan aiki.”
Hukumar ta kuma wallafa cikakken jerin bankunan da abin ya shafa da kuma sabbin bankunan da suka gaje su, wanda ya shafi jihohi da dama kamar Lagos, Anambra, Kano, Rivers da kuma Babban Birnin Tarayya (FCT).
Daga cikin bankunan da aka ambata akwai Mouau Vasmucs Microfinance Bank, Eduek Microfinance Bank, Ini Microfinance Bank, Nsehe Microfinance Bank, Awka Microfinance Bank, da Enugwu-Ukwu Microfinance Bank, da sauransu da dama.
Tsarin P&A na bai wa bankuna masu karfi damar karbar ajiyar kudi da wasu basussuka na bankunan da suka gaza, domin tabbatar da ci gaba da hidima ga kwastomomi tare da kare masu ajiya.
Masana sun bayyana cewa wannan mataki na nuna muhimmiyar rawar da NDIC ke takawa wajen tabbatar da daidaiton harkokin kudi a kasar, amma sun jaddada bukatar karin kulawa da inganta tsarin shugabanci domin hana sake faruwar gazawar bankuna a nan gaba.
