Matatar man fetur ta Dangote ta fitar da kusan lita miliyan 434 na fetur zuwa ƙasashen waje a watan Maris na shekarar 2026, bayan da ta samar da man da ya wuce bukatar cikin gida, a cewar bayanan Hukumar Kula da Harkokin Mai ta Najeriya (NMDPRA).
Rahoton ya nuna cewa matatar ta samar da jimillar lita biliyan 1.49 a cikin watan, inda aka samar da lita biliyan 1.06 don amfani a cikin gida, sannan aka fitar da ragowar zuwa ƙasashen waje.
Ana gudanar da aikin matatar a matakin amfani da kashi 93.62 cikin 100 na ƙarfin ta, lamarin da ya tabbatar da matsayin ta a matsayin babbar mai samar da kayayyakin mai a Najeriya.
A matsakaici, matatar na samar da lita miliyan 48.2 a kullum, inda ake samar da lita miliyan 34.2 don kasuwar cikin gida. Fitar da fetur zuwa ƙasashen waje na nuna wani babban sauyi a bangaren kasuwancin mai na ƙasa, wanda a baya ya dogara da shigo da mai daga waje.
A wata sanarwa da matatar ta fitar, ta ce: “Najeriya ta samu wani tarihi a watan Maris, inda ta zama mai fitar da man fetur zuwa ƙasashen waje karo na farko.”
Bayanan kasuwa sun nuna cewa shigo da fetur daga ƙasashen waje ya ragu zuwa ganga 41,000 a rana, mafi ƙanƙanta da aka taɓa samu, yayin da samar da ɗanyen mai ga matatar Dangote ya karu zuwa ganga 565,000 a rana, wanda ya ƙara yawan samarwa.
Jimillar fitar da mai zuwa waje ta kai ganga 44,000 a rana, ciki har da jigilar ganga 317,000 zuwa ƙasar Mozambique, wanda ya zama karo na farko da matatar ta kai kaya Gabashin Afirka.
Haka kuma, matatar Dangote ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da dizal, inda take samar da lita miliyan 16.5 a kullum, amma daga ciki lita miliyan 2.2 ne kawai ake samarwa cikin gida, yayin da mafi yawancin ake fitarwa zuwa ƙasashen waje.
A gefe guda, matatun mai na gwamnati sun ci gaba da kasancewa a rufe. Matatun Fatakwal, Warri da Kaduna ba sa aiki, yayin da ƙananan matatun mai kamar Walter Smith, Edo da Aradel ke samar da kimanin lita miliyan 0.629 na dizal a kullum kawai.
Masana sun bayyana cewa ƙara ƙarfin aikin matatar Dangote na sauya fasalin harkar mai a Najeriya, inda ƙasar ke kan hanyar zama mai fitar da kayayyakin mai. Sai dai sun jaddada cewa, dole ne a tabbatar da wadataccen ɗanyen mai, ingantaccen tsarin rarraba mai, da kuma farfaɗo da matatun gwamnati domin cimma cikakkiyar dogaro da kai a fannin makamashi.
