Hauhawar farashin abinci a Najeriya ta karu zuwa kashi 12.12 cikin 100 a watan Fabrairu na 2026, lamarin da ya kawo karshen saukar da ta yi zuwa kasa da kashi 10 a watan Janairu, tare da nuna sabon matsin lamba kan kudin abincin al’umma.
A cewar National Bureau of Statistics (NBS), adadin ya tashi daga kashi 8.89 a watan Janairu, wanda ke nuna karin maki 3.23 cikin 100.
Rahoton ya bayyana cewa, “Hauhawar farashin abinci a watan Fabrairu 2026 ya kai kashi 12.12… amma ya ragu da maki 14.86 idan aka kwatanta da watan Fabrairu 2025 wanda ya kai kashi 26.98.”
A ma’aunin wata zuwa wata, farashin abinci ya karu da kashi 4.69, sakamakon tsadar kayan masarufi irin su wake, rogo, garin doya, kifi busasshe (crayfish), garin gero da kuma wake iri-iri. Manoma sun danganta wannan karuwa da tsadar kayan noma, tare da kira ga gwamnati da ta dauki mataki.
Duk da wannan karin na baya-bayan nan, alkaluman na dogon lokaci sun nuna sauki idan aka kwatanta da bara, inda matsakaicin hauhawar farashin abinci na shekara ya tsaya a kashi 19.08, daga kashi 37.40 a watan Fabrairu 2025.
Bayanan jihohi sun nuna bambanci mai yawa: Jihar Kogi (26.91%), Adamawa (23.12%), da Benue (21.89%) su ne ke da mafi girman hauhawar farashin abinci, yayin da Katsina (5.09%), Bauchi (7.09%), da Imo (7.65%) suka fi karanci.
Hauhawar farashin kaya gaba daya (headline inflation) ta dan sauka zuwa kashi 15.06 a watan Fabrairu daga kashi 15.10 a watan Janairu, duk da cewa a ma’aunin wata zuwa wata ta karu da kashi 2.01, wanda ke nuna ci gaba da matsin lamba kan farashi.
Bangaren abinci da abin sha marasa giya ne suka fi bada gudunmawa ga hauhawar farashin gaba daya da maki 6.03.
Shugabannin kasuwanci sun gargadi cewa wannan dan saukar da aka samu ba ya kawo sauki sosai. Femi Egbesola na kungiyar Association of Small Business Owners ya ce, “A gare mu ‘yan kasuwa kanana da matsakaita, wannan ba lokaci ba ne na murna… farashin abinci da makamashi har yanzu suna da tsada.”
Shi ma masani kan tattalin arziki, Muda Yusuf, ya bayyana damuwarsa kan dawowar hauhawar farashin abinci zuwa sama da kashi 10, yana mai danganta hakan da matsalolin tsaro, tsadar sufuri da kuma hauhawar farashin makamashi.
“Idan hauhawar farashin abinci ta tashi daga kasa da kashi 10 zuwa kusan kashi 12, to wannan abin damuwa ne,” in ji shi.



