Gwamnatin Tarayya na Tura Shirin Gas na Dala Biliyan 20 Zuwa Turai

Gwamnatin Tarayya ta kara kaimi wajen aiwatar da wani shiri na gina bututun iskar gas na dala biliyan 20, wanda zai rika kai gas daga Najeriya zuwa kasuwannin Turai.

Shirin, wanda har yanzu yana matakin farko na tsarawa, na gudana ne karkashin hadin gwiwar wasu manyan kamfanonin duniya, kuma ana sa ran zai bi matakai masu tsauri na fasaha, kasuwanci da kuma dokoki kafin fara aiki.

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur (Gas), Ekperikpe Ekpo, ya gana da masu ruwa da tsaki a birnin London, inda ya bayyana tattaunawar a matsayin “mai muhimmanci kuma ta tarihi.” Ya ce: “Najeriya na shirin bai wa masu zuba jari damar cin gajiyar wannan arzikin gas… dole ne mu kasance da niyya wajen amfani da albarkatunmu.”

An tsara cewa bututun zai rika daukar kusan biliyan 30 na cubic metres na gas a duk shekara, yana tasowa daga ma’adinan kudancin Najeriya, ya bi ta kasar Chadi da Libya, sannan ya shiga karkashin teku zuwa Sicily a kasar Italiya, kafin ya wuce zuwa sauran kasashen Turai.

Babban Mataimakin Shugaban NNPC Limited mai kula da Gas, Wutar Lantarki da Sabbin Hanyoyin Makamashi, Olalekan Ogunleye, ya tabbatar da cewa manufofi da shirye-shiryen zuba jari sun daidaita. Ya ce: “NNPCL a shirye take domin kasuwanci… muna mayar da hankali wajen samar da damar zuba jari, kawar da cikas, da kuma hada hannu da ingantattun masu zuba jari.”

Jagoran aikin, Roger Tamraz, Shugaban Kamfanin Netoil Inc., ya bayyana bututun a matsayin muhimmin ginshiki ga makomar makamashin Turai, yana mai cewa akwai bukata mai yawa da kuma hanyoyin samar da kudaden gudanar da aikin.

Sauran abokan hadin gwiwa, ciki har da Shugaban Unicorn, Alain Bolo, sun jaddada cewa aikin zai taimaka wajen rage konewar gas a banza tare da mayar da Najeriya babbar mai samar da gas a duniya.

Daraktan aikin na Netoil, Henry Erimodafe, ya bayyana shirin a matsayin “nasara ga kowa,” wanda zai samar da ayyukan yi, jawo jari, da kuma samar da riba mai dorewa ga Najeriya da sauran abokan hulda.

Masu ruwa da tsaki na ganin cewa wannan bututun zai iya sauya matsayin Najeriya a kasuwar makamashi ta duniya, ya kara karfafa dangantaka da Turai, tare da tallafawa tsaron makamashi na dogon lokaci da kuma bunkasa tattalin arziki.