Farashin gas na girki a Najeriya ya tashi zuwa kusan ₦1,400 kan kowanne kilo, sakamakon hauhawar farashin makamashi a kasuwannin duniya, lamarin da ke ƙara matsa wa gidaje da ƙananan ‘yan kasuwa.
Rahotanni daga masu ruwa da tsaki a masana’antar gas da kuma binciken kasuwa sun nuna cewa farashin Liquefied Petroleum Gas (LPG), wanda aka fi sani da gas na girki, a matakin ex-depot ya karu zuwa kusan ₦18 miliyan kan tan 20 (20MT) a wannan makon. Wannan ya nuna ƙaruwa daga kusan ₦15.95 miliyan da ake sayarwa mako guda da ya gabata.
Wannan hauhawar farashin na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin siyasa da na tsaro tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran ke haifar da tangarda a samarwa da kuma hanyoyin rarraba man fetur da iskar gas a kasuwannin duniya, wanda hakan ke jawo tashin farashin kayayyakin makamashi a sassa daban-daban na duniya.
Najeriya, wadda har yanzu tana shigo da wani ɓangare na gas na girki daga ƙasashen waje, na fuskantar tasirin wannan sauyi cikin gaggawa, lamarin da ya sa farashin cikin gida ya fara hawa.
A wasu wuraren sayar da gas a Lagos, farashin gas na girki a matakin dillanci ya kai har ₦1,400 kan kilo, abin da ke ƙara nauyi ga kasafin kuɗin gidaje, musamman a lokacin da tsadar rayuwa ke ci gaba da ƙaruwa.
Masu harkar gas sun ce wasu manyan depots ma sun bayyana farashi har zuwa ₦19 miliyan kan tan 20, yayin da wasu ke sayarwa a kusan ₦17.5 miliyan, abin da ke nuna bambancin farashi a kasuwa.
Masana sun bayyana cewa duk da cewa Najeriya na samar da adadi mai yawa na gas na girki a cikin gida, farashin da ake bi a kasuwannin duniya na da tasiri sosai wajen ƙayyade farashin cikin gida. Saboda haka, duk lokacin da farashin mai da gas ya tashi a duniya, dillalan cikin gida kan ɗora ƙarin farashin ga masu amfani.
Hauhawar farashin gas na girki na zuwa ne a lokacin da sauran farashin makamashi ma ke ƙaruwa. Rahotanni na baya-bayan nan sun nuna cewa farashin fetur da dizel ma sun fara hawa sakamakon tashin farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Masana tattalin arziki sun yi gargadin cewa idan farashin ya ci gaba da kasancewa a sama, hakan na iya ƙara tsananta matsin tattalin arziki ga iyalai da ƙananan ‘yan kasuwa da ke dogaro da gas wajen girki da sauran ayyukan yau da kullum.
Wasu masu ruwa da tsaki a harkar gas sun bukaci masu amfani da su rika miƙa koken su ga masu tsara manufofi na gwamnati maimakon masu gidajen sayar da gas, suna mai cewa hauhawar farashin na da alaƙa da yanayin kasuwannin duniya fiye da matsalar samarwa a cikin gida.
A halin yanzu, yayin da rikicin Gabas ta Tsakiya ke ci gaba da ta’azzara tare da rikicewar kasuwannin makamashi, masana na hasashen cewa farashin gas na iya ci gaba da kasancewa a sama na wani lokaci, lamarin da ka iya sa wasu gidaje rage amfani da gas ko kuma komawa wasu hanyoyin girki na dabam.

