Jihohi 12 Sun Zartar da Dokar Daidaita Haraji – Oyedele

Taiwo Oyedele ya bayyana cewa aƙalla jihohi 12 a Najeriya sun riga sun zartar da dokar daidaita tsarin haraji (Tax Harmonisation Law).

Oyedele ya ce wasu jihohi 13 kuma sun gabatar da kudirin dokar ga majalisun dokokin jihohinsu, yayin da sauran jihohin ke kan matakai daban-daban na aiwatar da wannan tsari.

Ya bayyana cewa dokar na cikin shirin gyaran haraji na gwamnatin Bola Tinubu, wanda ke da nufin sabunta tsarin kudaden shiga na ƙasa, tallafa wa ci gaban kasuwanci, tare da kare marasa ƙarfi a cikin al’umma.
Oyedele ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin bikin kammala horo na ’yan kasuwa 5,900 da gidauniyar MTN Foundation ta horas.

A cewarsa, manufar dokar ita ce kawar da haraji marasa amfani da kuma dakile cin zarafin jama’a da wasu masu karɓar haraji ke yi.

Ya ƙara da cewa dokar za ta sauƙaƙa tsarin haraji, ta kare haƙƙin masu biyan haraji, tare da magance rashin adalci a tsarin karɓar haraji.

Oyedele ya ce: “Bayyananniyar hanya, ladabtar da kashe kuɗi, alhaki da kuma gaskiya su ne ginshiƙai masu muhimmanci wajen gina ingantaccen tsarin haraji.”

A baya, Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan dokokin gyaran haraji guda huɗu a ranar 26 ga Yuni, 2025, inda ya jaddada cewa manufar gyaran ba wai ƙara yawan haraji ba ne, sai dai sake fasalin tsarin tattalin arziki da kuma ƙarfafa yarjejeniyar zamantakewa tsakanin gwamnati da jama’a.

Shugaban ya kuma bayyana cewa dokokin daidaita haraji za su ƙara wa gwamnati ƙarfi wajen samar da kuɗaɗen gina manyan ayyukan more rayuwa, tare da rage maimaituwa da rashin inganci a tattara kuɗaɗen shiga.

Masana tattalin arziki na cewa idan aka aiwatar da waɗannan gyare-gyare a dukkan jihohin Najeriya, hakan na iya inganta sauƙin gudanar da kasuwanci tare da ƙara amincewar masu zuba jari a tattalin arzikin ƙasar.