Matatar mai ta Dangote Petroleum Refinery ta kara farashin sayar da fetur (Premium Motor Spirit – PMS) a matakin gantry zuwa N1,175 a kowace lita, wanda ya zama karo na uku da aka kara farashin cikin mako guda.
Matatar ta sanar da wannan karin farashi ga ‘yan kasuwar mai a ranar Litinin, inda aka daga farashin daga N995 a kowace lita da aka sanar ranar Juma’a zuwa N1,175 a kowace lita, wanda ke nuna karin N180 ko kusan kashi 18.1 cikin dari cikin kwanaki uku kacal.
Wani jami’i daga matatar ya ce:
“Eh, an sake duba farashin gantry.
Yanzu PMS ya kai N1,175 a lita, yayin da Automotive Gas Oil (AGO) wato dizal ya kai N1,620 a lita. Kasuwar ta yi matukar rikicewa a ‘yan kwanakin nan, kuma kudin maye gurbin kaya ya karu sosai. Sabbin farashin nan sun yi daidai da halin kasuwa da kuma yanayin kudaden da muke fuskanta a yanzu.”
Wannan ci gaba ya zo ne bayan da matatar ta dakatar da lodin fetur na wani lokaci tare da takaita fitar da tankokin mai, lamarin da ya haifar da rade-radin cewa za a sake kara farashin.
Sabon karin farashin shi ne karo na hudu da aka sake duba farashin cikin kasa da makonni biyu, abin da ke nuna matsin lamba da ake fuskanta a kasuwar man fetur ta Najeriya, musamman sakamakon sauye-sauyen farashin mai a kasuwannin duniya.
Da wannan sabon tsarin, farashin N1,175 a lita ya yi tsalle mai yawa idan aka kwatanta da farashin N995 a lita da ake sayarwa a baya.
Ana sa ran direbobi da masu amfani da man fetur za su fara sayen fetur a gidajen mai da farashin da ya haura N1,200 a kowace lita, lamarin da zai kara tsananta matsin tattalin arziki ga fasinjoji da sauran al’umma.
A halin da ake ciki, Kungiyar Masu Gidajen Sayar da Man Fetur ta Najeriya (PETROAN) ta yi gargadin cewa farashin fetur a gidajen mai na iya kaiwa N2,000 a kowace lita, sakamakon rikicin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban PETROAN na kasa, Billy Gillis-Harry, ya bukaci Kamfanin Mai na Kasa (NNPCL) da ya gaggauta karfafa matatun mai na cikin gida domin kare Najeriya daga tasirin sauye-sauyen kasuwar mai ta duniya.
Ya ce:
“Kafin rikicin ya fara, ana sayar da fetur a kusan N774 a lita, amma yanzu ya wuce N1,000 a lita, wanda ke nuna karin kusan kashi 30 cikin dari. Haka kuma dizal (AGO) da ake sayarwa a kusan N950 a lita a baya yanzu ya haura N1,400 a lita.”
Gillis-Harry ya kara da cewa idan halin da ake ciki ya ci gaba, fetur na iya kaiwa kusan N2,000 a kowace lita, yayin da dizal zai iya kusantar N3,000 a kowace lita.

