Kamfanin Mai na Kasa, Nigerian National Petroleum Company Limited, ya samu raguwar kudaden shiga sosai a watan Janairu na shekarar 2026, inda kudaden da ya samu suka ragu zuwa N2.57 tiriliyan, idan aka kwatanta da N4.82 tiriliyan da aka samu a watan Disambar 2025.
An bayyana wannan a cikin takaitaccen rahoton wata-wata na kamfanin na Janairu 2026, wanda ya nuna cewa kudaden shiga sun ragu matuka duk da cewa an samu dan karamin karin ribar da ta rage bayan biyan haraji.
Rahoton ya ce ayyukan gas na kamfanin sun ci gaba da tafiya yadda ya kamata a lokacin, wanda ya taimaka wajen samar da wani dan kwanciyar hankali duk da raguwar kudaden shiga.
A cewar rahoton:
“NNPC Ltd ta lura cewa harkokin gas sun kasance cikin daidaito a wannan lokaci. Samar da gas ya kai biliyan 7.283 na cubic feet a kowace rana, yayin da sayar da gas ya kai biliyan 4.978 na cubic feet a rana a watan Janairu.”
Rahoton ya kuma nuna cewa ribar kamfanin bayan biyan haraji ta dan karu kadan duk da raguwar kudaden shiga da kuma kudaden da aka mika wa gwamnati.
Rahoton ya kara da cewa samar da mai ya karu idan aka kwatanta da watan da ya gabata, bayan kammala aikin gyaran manyan wuraren samar da mai a Agbami Oil Field da kuma Renaissance (Estuary Area).
Sai dai kuma, rahoton ya nuna cewa isar da mai da aka tsara yi a watan Janairu ta fuskanci matsaloli sakamakon mummunan yanayi, matsalolin fitar da kaya, da kuma kalubalen kula da kayayyakin aiki.
Masana sun ce wannan ya nuna yadda bangaren mai da gas ke matukar dogaro da sauye-sauyen farashin danyen mai a kasuwar duniya, da kuma matakin samarwa a cikin gida da sauran matsalolin aiki.
NNPC Ltd ta kuma bayar da sabbin bayanai kan manyan ayyukan bututun gas da ake ginawa domin karfafa samar da gas a cikin gida da kuma tallafa wa bunkasar masana’antu.
Daga cikin manyan ayyukan akwai Ajaokuta-Kaduna-Kano Gas Pipeline Project da kuma Obiafu-Obrikom-Oben Gas Pipeline, wadanda ake sa ran za su kara karfin tsarin gas na Najeriya tare da tabbatar da wadataccen gas ga masana’antu da kuma amfani na cikin gida.
Rahoton ya ce aikin ya kai kashi 96 cikin dari na kammalawa, yayin da aikin hako bututu a mahadar Kogin Neja (River Niger) ke ci gaba da tafiya yadda ya kamata.
Duk da wannan raguwar kudaden shiga a watan Janairu 2026, NNPC Ltd ta ci gaba da kasancewa daya daga cikin manyan masu kawo kudaden shiga ga gwamnati.
Daga Janairu zuwa Disambar 2025, kamfanin ya mika wa gwamnatin tarayya N14.706 tiriliyan ta hanyar haraji, kudaden sarauta (royalties), da sauran kudaden doka.
A watan Disamba, Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da soke wani babban bangare na bashin da NNPC Ltd ke bin Asusun Tarayya (Federation Account), inda aka goge kusan dala biliyan 1.42 da kuma N5.57 tiriliyan na bashin kamfanin.
