Cunkoso: Tinubu Ya Bada Umurnin Dakatar da Sabon Tsarin Biyan Kuɗi na FAAN

Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya ba da umarnin dakatar da tsarin biyan kuɗi ba da tsabar kuɗi ba (cashless) na Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Najeriya (FAAN), bayan da tsarin ya haddasa mummunan cunkoson ababen hawa a filayen jiragen sama a faɗin ƙasar.

Ministan Sufurin Jiragen Sama da Sararin Samaniya, Festus Keyamo, ne ya sanar da hakan yayin ganawarsa da manema labarai bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da shugaban ƙasa ya jagoranta.

An fara aiwatar da tsarin ne a ranar 1 ga Maris, inda aka wajabta biyan kuɗaɗe ta hanyar kati ko na’urorin POS a ƙofofin shiga filayen jirage, wuraren ajiye motoci da dakunan tarbar baƙi (lounges), lamarin da ya kawo ƙarshen karɓar kuɗi ta hannu da aka shafe sama da shekaru 50 ana yi.

Sai dai cikin ‘yan kwanaki kaɗan da fara aiwatarwa, an samu ruɗani da cunkoso a manyan filayen jiragen sama, ciki har da Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas da kuma Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, inda direbobi suka fuskanci dogayen layuka, yayin da wasu fasinjoji suka rasa jiragensu.

“A fannin sufurin jiragen sama, abubuwa biyu masu muhimmanci sun taso a yau,” in ji Keyamo. “Na farko shi ne tsarin cashless da muka ƙaddamar a ƙofofin karɓar kuɗi a faɗin ƙasa domin kawar da cin hanci da kuma inganta kuɗaɗen shiga na Gwamnatin Tarayya.”

Ya amince cewa sabon tsarin ya haifar da babbar tangarda. “Da fara aiwatar da tsarin kasa da mako guda, ya haifar da cunkoso mai yawa a faɗin ƙasar,” in ji shi.

A cewarsa, Shugaba Tinubu ya shiga lamarin ne saboda damuwarsa kan wahalhalun da jama’a ke fuskanta.
“Shugaban ƙasa ya damu matuƙa da lafiyar ‘yan Najeriya da kuma yadda mutane da dama ke rasa jiragensu.

Saboda tausayi, ya ba da umarnin a dakatar da tsarin na yanzu saboda wahalar da jama’a ke sha,” in ji Keyamo.
Ministan ya bayyana cewa FAAN za ta koma karɓar kuɗi ta hannu na ɗan lokaci, tare da amfani da tsarin haɗaka (hybrid) ga waɗanda suka riga suka mallaki katin FAAN.

“Za mu samar da tsarin da za mu riƙa karɓar kuɗi ta hannu na ɗan lokaci, sannan mu ci gaba da amfani da katunan da aka riga aka bayar,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa gwamnati za ta nemi haɗin gwiwar ɓangaren masu zaman kansu domin tsara ingantaccen tsarin biyan kuɗi na lantarki.

“Shugaban ƙasa ya ce ko da za a biya kwamishin, za mu haɗa da ɓangaren masu zaman kansu domin samar da tsarin da zai fi inganci wanda har yanzu zai kawar da karɓar kuɗi ta hannu,” in ji shi.

Keyamo ya jaddada cewa dakatarwar ba yana nufin gwamnati ta yi watsi da tsarin cashless ba ne, illa dai mataki ne na rage wahalar da jama’a ke sha.
“Ba wai shugaban ƙasa yana farin ciki da komawa tsarin kuɗi ta hannu ba ne. Mataki ne na tausayi domin rage wahalar da ‘yan Najeriya ke fuskanta a halin yanzu,” in ji shi.