Trends

Yakin Isra’ila da Iran: Kamfanonin Jiragen Sama Sun Yi Asarar N7.5Bn

NCAA NCAA

Kamfanonin jiragen sama na ƙasashen waje da ke zirga-zirga tsakanin Najeriya da Gabas ta Tsakiya sun yi asarar sama da Naira biliyan 7.5 bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran ya haddasa rufe sararin samaniya da kuma dakatar da tashi da saukar jirage.

Bincike ya nuna cewa kamfanonin Emirates da Qatar Airways, waɗanda ke gudanar da zirga-zirga kullum daga Legas zuwa Dubai da Doha, sun kasa gudanar da jiragansu yayin da rikicin ya tsananta, lamarin da ya jefa jirage a ƙasa tare da haddasa tangarda ga fasinjoji.

Kamfanin Emirates ya shirya amfani da jirginsa kirar Boeing 777-300ER mai ɗaukar fasinjoji tsakanin 354 zuwa 360, yayin da Qatar Airways ta tanadi Boeing 787-800 mai ɗaukar fasinjoji tsakanin 210 zuwa 250. A haɗe, kimanin fasinjoji 560 ne abin ya shafa a kowace tafiya.

Da aka yi amfani da kiyasin kuɗin tikiti mafi ƙanƙanta — Naira miliyan 1.3 na Qatar Airways da dala $1,380 (kimanin Naira miliyan 1.9) na Emirates — ana hasashen kamfanonin sun yi asarar Naira biliyan 7.53 tsakanin ranar Asabar da Talata.

Wasu daga cikin fasinjojin da abin ya shafa sun bayyana takaicinsu kan yadda suka rasa muhimman al’amuran kasuwanci da na rayuwa. Wani fasinja da ya makale, Dare Olanihun, ya ce: “Hawaye suka zubo min lokacin da aka ce mu sauka daga jirgi a yammacin Asabar. Wannan tafiya za ta yi matuƙar tasiri a rayuwata ta sana’a.”

Rikicin ya biyo bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran, inda aka kashe Jagoran Addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, lamarin da ya jawo Iran ta mayar da martani da harba makamai masu linzami zuwa Isra’ila da sansanonin Amurka da ke Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Kasashe da dama ciki har da Syria, Jordan, Kuwait da Rasha sun sanar da rufe sararinsu ga zirga-zirga, abin da ya ƙara dagula harkokin sufurin jiragen sama.

Tasirin rikicin ya kuma shafi kamfanonin samar da abinci a filayen jiragen sama, waɗanda suka amfana daga umarnin da ya wajabta wa kamfanonin jiragen sama na ƙasashen waje su riƙa amfani da masu samar da abinci na cikin gida.

Da aka dakatar da jirage, masu samar da abincin sun bayyana cewa sun yi asara tare da lalacewar wasu kayayyakin abinci, yayin da wasu ke nuna damuwa kan halin da ‘yan uwansu ke ciki a ƙasashen da rikicin ya shafa.