Farashin man fetur a kasuwannin duniya ya tashi jiya, inda man Brent ya kai dala 82 kan kowanne ganga, yayin da WTI ya sayu kan dala 70.91. Wannan ya biyo bayan hare-haren da aka kai wa jiragen ruwa a kusa da mashigar tekun Strait of Hormuz. Masana sun yi gargadin cewa idan rikicin ya ci gaba, farashin na iya haura dala 100 kan ganga.
Rikicin ya ƙara tsananta bayan Saudiyya ta rufe babbar matatar man fetur ɗinta ta Ras Tanura sakamakon harin jirgin sama mara matuƙi (drone). Wani kakakin ma’aikatar tsaro ya shaida wa Al Arabiya cewa, “Ƙurar da ta faɗo daga jiragen da aka tare ta haddasa ƙaramin gobara,” yana mai ƙara da cewa ba a samu asarar rai ba.
Kamfanin Chevron ya dakatar da ayyukansa a filin iskar gas na Leviathan a Isra’ila, yayin da kamfanin Energean ya dakatar da samarwa a wasu ƙananan filayen da ke teku, lamarin da ya rage fitar da iskar gas zuwa Masar.
Haka kuma, zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Strait of Hormuz — wadda ke ɗaukar kusan kashi ɗaya bisa biyar na man da ake jigila a duniya — ta ragu sosai.
Cibiyar Bincike da Ƙarfafa Harkokin Ruwa (SEREC) ta yi gargaɗin cewa kuɗin jigilar kaya ta ruwa na iya ƙaruwa da kashi 40 cikin 100, yayin da kuɗin inshorar haɗarin yaƙi zai iya ninka har sau huɗu.
Shugaban Bincike na SEREC, Eugene Nweke, ya ce, “Rikicin Amurka da Iran ba wai rikicin siyasa kawai ba ne, jarabawa ce ga tsarin kasuwancin duniya baki ɗaya.”
Binciken da cibiyar ta yi ya nuna cewa kuɗin inshorar jiragen ruwa na iya tashi da kashi 200 zuwa 400 cikin 100, wanda hakan zai tilasta wa jiragen ruwa sauya hanya su bi ta Cape of Good Hope.
Wannan sauyin hanya zai ƙara kwanaki da ɗaruruwan dubban daloli a kuɗin jigila, tare da tasirin da zai shafi tattalin arziƙin ƙasashe daban-daban.
Ga Nijeriya, rikicin na tattare da haɗari da kuma dama. Tashin farashin man fetur na iya samar wa ƙasar ƙarin dala biliyan 18 zuwa 22 a shekara, tare da haɓaka ci gaban tattalin arziƙi (GDP) da kashi 1.2 cikin 100. Sai dai SEREC ta yi gargaɗin cewa hauhawar farashi na iya ƙaruwa da kashi 3 zuwa 5 idan ba a kiyaye tsauraran matakan kashe kuɗi ba.
An bayyana Matatar Dangote da ke Legas a matsayin wata muhimmiyar kariya ga tattalin arziƙin ƙasa. SEREC ta ce, “Idan aka sarrafa ta yadda ya kamata, matatar za ta zama ginshiƙin daidaita tattalin arziƙin ƙasa a lokacin girgizar tattalin arziƙi daga waje,” tana mai nuna cewa za ta rage dogaro da shigo da mai daga ƙasashen waje tare da sauƙaƙa matsin lamba kan naira.
SEREC ta buƙaci gwamnatocin Afirka da su zuba ribar da za su samu daga tashin farashin mai cikin asusun daidaita tattalin arziƙi, su faɗaɗa ajiyar mai na gaggawa, tare da ƙarfafa tsaron teku.
A ƙarshe, Nweke ya ce, “Ƙarfin Nijeriya ba zai dogara kawai da ƙarin kuɗaɗen da za ta samu daga man fetur ba, sai dai kan tsauraran matakan sarrafa kuɗi, inganta tace mai a gida, faɗaɗa kasuwanci, da ƙarfafa gasa a harkokin teku.”
