Trends

Karfafa Matatun Mai na Cikin Gida ya Zama Dole – PETROAN

Ƙungiyar Masu Gidajen Sayar da Man Fetur ta Nijeriya (PETROAN) ta sake kira ga gwamnatin ƙasa da ta ƙarfafa matatun mai na cikin gida, tana mai danganta hakan da tsanantar rikicin Gabas ta Tsakiya da tasirinsa kan kasuwar man fetur ta duniya.

Shugaban Ƙasa na PETROAN, Dakta Billy Gillis-Harry, ya ce, “Haɗa kai da ƙarfafa matatun mai na Nijeriya ta hanyar tabbatar da wadataccen ɗanyen mai abu ne na gaggawa.”

Ya yi gargadin cewa girgizar tattalin arziƙi daga ƙasashen waje na iya dagula farashin man fetur a cikin gida da kuma kasuwar canjin kuɗi.

Ƙungiyar ta nuna damuwa kan ƙarin tashin hankali na soja da ya shafi Amurka, Iran, Isra’ila da ƙawayensu, tana mai cewa rikicin ya kawo cikas ga tsarin samar da makamashi a duniya. Gillis-Harry ya ce, “Wannan rikicin siyasa ya girgiza kasuwannin makamashi sosai.”

A wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na PETROAN, Dakta Joseph Obele, ya fitar, an jaddada muhimmancin mashigar tekun Strait of Hormuz, wadda kusan kashi 20 cikin 100 na jigilar ɗanyen mai da iskar LNG na duniya ke bi ta cikinta.

Sanarwar ta ce hare-haren baya-bayan nan sun dakatar da ayyuka a matatar Ras Tanura ta Saudiyya tare da dakatar da samar da LNG a Qatar, lamarin da ya sa farashin iskar gas a Turai ya tashi da kashi 50 cikin 100.

Farashin man Brent ya tashi kusa da dala 80 kan ganga, inda masana ke gargadin cewa zai iya haura dala 100 idan rikicin ya ci gaba. PETROAN ta jaddada cewa dogaro da shigo da man da aka tace daga ƙasashen waje ya sa kasuwar cikin gida ta Nijeriya cikin haɗari.

Sanarwar ta kuma yaba wa Dokar Shugaban Ƙasa ta 9 da ta tilasta wa NNPCL tura kuɗaɗen shiga kai tsaye. Gillis-Harry ya bayyana matakin a matsayin “shawara mai ƙarfin hali da ta dace da ingantattun ƙa’idojin duniya.”
Ya kuma yaba wa Shugaban NNPCL, Bayo Ojulari, kan ƙoƙarinsa na farfaɗo da Matatar Fatakwal (Port Harcourt Refinery), ciki har da tattaunawa da wata kamfanin fasaha daga ƙasar Sin.

Gillis-Harry ya goyi bayan amfani da tsarin kamfanin Nigeria LNG na Bonny a matsayin abin koyi, yana mai cewa hakan zai “ƙara inganci, gaskiya, da bin ƙa’idojin kasuwanci na kamfanoni masu zaman kansu.”

Ya ƙara da cewa, “Amfani da tsarin gudanarwa mai dogaro da kasuwanci irin na NLNG zai sa matatun mai su zama masu riba, inganci, kuma masu iya gogayya a duniya.”

A ƙarshe, ya jaddada cewa PETROAN a shirye take ta yi aiki tare da gwamnati domin ƙarfafa tsaron makamashi da rage dogaro da shigo da mai daga waje.