Tinubu Ya Nada Tunji Disu Masayin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda

Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba ya kaddamar da Olatunji Disu a matsayin Mukaddashin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda (IGP) a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

An gudanar da bikin, wanda ya fara misalin karfe 4:00 na yamma, tare da halartar manyan jami’an gwamnati da suka hada da Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu; Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila; Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume; da tsohon IGP, Kayode Egbetokun.

Shugaba Tinubu ya dora sabbin alamun mukami a jikin Disu tare da yabawa Egbetokun bisa hidimar da ya yi wa kasa. Ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa kan kwarewa da gogewar Disu wajen jagorantar Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya a wannan lokaci na kalubalen tsaro.

Nadin Disu ya biyo bayan murabus din Egbetokun, wanda ya mika a ranar Talata kuma Shugaban Kasa ya amince da shi nan take. Mai ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya ce tsohon IGP din ya bayyana dalilan iyali masu muhimmanci a matsayin hujjar sauka daga mukamin.

Sai dai wasu majiyoyi daga Fadar Shugaban Kasa sun ce an bukaci Egbetokun ya sauka ne bayan ganawa ta sirri da Shugaban Kasa a daren Litinin.

Disu, wanda aka haifa ranar 13 ga Afrilu, 1966, zai kai shekarun ritaya na dole (shekara 60) a ranar 13 ga Afrilu, 2026. Sai dai gyaran Dokar ‘Yan Sanda ya bai wa IGP damar yin cikakken wa’adi na shekaru hudu ko da ya kai shekarun ritaya, idan aka tabbatar da shi a matsayin cikakken IGP.

Disu ya shiga aikin ‘yan sanda tun 1992, kuma ya taba rike mukaman Kwamandan Rapid Response Squad (RRS) a Legas, Kwamishinan ‘Yan Sanda a Babban Birnin Tarayya (FCT), da Shugaban FCID Annex a Legas.

Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana nadin Disu a matsayin wanda ya dace, yana mai yabawa kwarewarsa da jajircewarsa a aikin tabbatar da doka da oda.

Disu zai ci gaba da rike mukamin ne a matsayin mukaddashi har sai Majalisar ‘Yan Sandan Najeriya ta tantance nadin, sannan Shugaban Kasa ya mika sunansa ga Majalisar Dattawa domin tabbatar da shi a matsayin cikakken Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, kamar yadda Dokar ‘Yan Sanda ta 2020 ta tanada.