Hukumar Kula da Kasuwar Hada-hadar Jari ta Najeriya (SEC) ta bayyana cewa gudunmawar kasuwar jari ga Jimillar Arzikin Cikin Gida (GDP) ta kai kashi 33%, yayin da jimillar darajar kasuwa ta karu zuwa Naira tiriliyan 123.93, daga Naira tiriliyan 55 a watan Afrilun 2024 – karin kaso 125%.
Daraktan Janar na Securities and Exchange Commission, Emomotimi Agama, ne ya bayyana hakan a jawabinsa na farko ga Kwamitin Aiki kan Inganta Ruwan Jari (Market Liquidity) a Legas. Ya bayyana ci gaban a matsayin tarihi, amma ya yi gargadin cewa dole ne a kara zurfafa ruwan jari domin dorewar nasarar.
Ya ce, “Tun daga Afrilu 2024, darajar kasuwa ta tashi daga kusan Naira tiriliyan 55 zuwa sama da Naira tiriliyan 123.93. Gudunmawarmu ga GDP ta karu daga kashi 13% zuwa 33%. Wadannan alkaluma na da kyau, amma ba su nuna cikakken labari ba.”
Agama ya jaddada cewa kasuwar jari mai karfi dole ne ta kasance mai saukin saye da sayarwa (liquid) domin ta zama ma’aunin lafiyar tattalin arziki. “Kasuwar jari ba caca ba ce; ita ce injin bunkasa kasa. Ita ce ke tallafa wa gina hanyoyi, samar da wutar lantarki ga masana’antu da kirkirar ayyukan yi,” in ji shi.
Duk da bunkasar, har yanzu akwai kalubale, inda harkar ciniki ta fi karkata ga wasu ‘yan kadan daga cikin manyan kamfanoni, lamarin da ke barin sauran hannayen jari ba su da yawan mu’amala. Haka kuma tsadar mu’amala na shafar manyan masu zuba jari, tare da rage kwarin gwiwa a kasuwa.
Don magance matsalolin, SEC ta kaddamar da kwamitin hadin gwiwa da ya hada da kasuwannin hada-hadar jari, masu rike takardun jari, manajojin asusun jari da ‘yan dillalai. Kwamitin zai duba tsarin ciniki da biyan kudi, tare da gabatar da gyare-gyare domin kara habaka ruwan jari da inganta tsarin biyan kudade.
Hukumar na kuma da burin jawo sabbin masu zuba jari kanana har miliyan 20 ta hanyar amfani da dandamali na zamani, sauya takardun jari zuwa tsarin dijital, da hadin gwiwa da kamfanonin fasahar kudi (fintech). Ana sa ran sabbin kayayyakin jari da suka hada da kwangilolin kariya (derivatives) za su kara fadada harkokin kasuwa.
Agama ya kuma bayyana cewa dokar Investments and Securities Act 2025 ta fadada ikon sa ido har zuwa kadarorin dijital, domin karkatar da mu’amalolin hasashe zuwa hanyoyin zuba jari da ke karkashin doka kuma masu amfani ga tattalin arziki.

