CBN da AU Sun Ci Gaba da Shirye-shiryen Kafa Bankin Tsakiyar Afirka

Najeriya ta samu kujera ta dindindin a Kwamitin Gudanarwa na Cibiyar Kudi ta Afirka (African Monetary Institute – AMI), lamarin da zai kara karfafa rawar da kasar ke takawa a kokarin hada kan tsarin kudi na nahiyar, a cewar Babban Bankin Najeriya (CBN).

An amince da hakan ne a zaman taro na 39 na Shugabannin Kasashen Tarayyar Afirka (AU Assembly) da aka gudanar a watan Fabrairu 2026, bayan Majalisar Zartarwa ta AU ta amince da kudurin.

AMI, wadda hedkwatarta ke Abuja, ita ce matakin farko kafin kafa Bankin Tsakiyar Afirka da ake shirin samarwa.
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya bayyana wannan ci gaba a matsayin “babban mataki a tafiyar hadin kan tsarin kudi na Afirka,” yana mai cewa hakan ya kara daukaka matsayin Najeriya a nahiyar.

Ya ce karbar bakuncin AMI, da kuma Bankin Tsakiyar Afirka a nan gaba, zai bai wa Najeriya damar taka muhimmiyar rawa wajen tsara tsarin kudin bai daya na Afirka, tare da sanya kasar a tsakiyar kokarin hada kan manufofin kudi.

Shugabannin kasashen AU sun amince da wakilcin dindindin na Najeriya a lokacin rikon kwarya (transitional phase), matakin da ake sa ran zai taimaka wajen inganta daidaiton manufofin tattalin arziki, hadin kan harkokin kudi, da kuma karfafa ikon kasashen Afirka kan tsarin kudinsu.

CBN ta yi aiki tare da Ma’aikatun Harkokin Waje, Shari’a, da Kudi domin samun wannan amincewa, inda ta jagoranci shirye-shiryen fasaha da suka samar da daftarin dokar AMI (Draft AMI Statute), tare da samar da wurin da cibiyar za ta fara aiki.

Cardoso ya ce amincin Najeriya a nahiyar ya karu sakamakon sauye-sauyen da aka yi wajen tabbatar da daidaiton kudi, kula da ajiyar waje, sa ido kan bankuna, da kuma sabunta tsarin biyan kudi. “A dunkule, nasarorin da aka samu sun kai wani sabon matsayi, abin da ke bayyana yadda martaba da tasirin Najeriya ke karuwa a nahiyar,” in ji shi.

Ya kara da cewa CBN za ta ci gaba da hada kai da hukumomin AU, kasashe mambobi, da sauran abokan hulda domin shimfida tubalin kafa Bankin Tsakiyar Afirka da kudin bai daya da ake shirin samarwa. Sai dai ya jaddada cewa kujerar dindindin ta Najeriya a Kwamitin AMI za ta kasance ne kawai a lokacin rikon kwarya, bisa ka’idojin AU na juyawa da daidaito tsakanin kasashe.