Hukumar Haraji Ta Kasa ta Kaddamar da Tsarin E-Invoicing Ga ‘Yan Kasuwa

Hukumar Haraji Ta Kasa (NRS) ta fara aiwatar da sabon tsarin fitar da takardun kudi ta yanar gizo (E-Invoicing) da kuma tsarin sa ido kan harkokin kasuwanci, domin karfafa tattara haraji, inganta gaskiya da kuma karfafa biyan haraji da son rai.

Shugaban Hukumar, Zacch Adedeji, ne ya sanar da kaddamar da shirin a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin. An sanya wa shirin suna Merchant Buyer Solution (MBS), kuma za a aiwatar da shi ne a matakai bisa rarrabuwar ‘yan kasuwa gwargwadon yawan kudaden shigar su na shekara.

Manyan ‘yan kasuwa ne suka fara amfani da tsarin, inda aka fara aiki da shi a hukumance tun ranar 1 ga Agustan 2025 bayan gwaji da aka gudanar a farkon shekarar. Daga bisani an tsawaita wa’adin aiwatarwa zuwa Nuwamban 2025 domin bai wa kamfanoni damar yin gyare-gyare na fasaha, kuma yawancin manyan masu biyan haraji sun fara aika bayanan takardun kudinsu cikin nasara.

Bisa wannan ci gaba, NRS za ta fadada tsarin zuwa matsakaitan ‘yan kasuwa masu juyin kudi tsakanin Naira biliyan 1 zuwa Naira biliyan 5 a shekarar 2026. An shirya kammala aiwatar da tsarin a watan Yuli na 2026, yayin da za a fara kakaba dokar bin sa a farkon shekarar 2027.

Ga kananan ‘yan kasuwa masu juyin kudi kasa da Naira biliyan 1, za a fara tuntuba da gwaji a shekarar 2027, tare da sa ran fara kakaba dokar bin tsarin a shekarar 2028.

Hukumar ta jaddada cewa shirin yana samun goyon bayan dokar Nigeria Tax Administration Act, wadda ta bai wa hukuma damar amfani da fasaha wajen gudanar da harkokin haraji, da kuma Nigeria Tax Act, wadda ta tanadi amfani da tsarin fiscalisation ga masu biyan haraji.

An shawarci ‘yan kasuwa da su tantance rukunin da suke ciki tare da shiga shirye-shiryen rajista da horo. NRS ta bayyana cewa kakaba dokar bin tsarin zai biyo bayan matakan tuntuba, gwaji da kuma bitar bayan fara aiki.

“Har yanzu Hukumar na nan daram wajen yin aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da sauyi mai sauki da kuma nasarar aiwatar da tsarin E-Invoicing,” in ji Adedeji.