Ma’aikatar Kiwon Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya, tare da Ofishin Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Kiwon Lafiyar Mata (OSSAP-WH), sun fara shirye-shiryen haɗa kai wajen aiwatar da tsare-tsare domin magance matsalolin da ke shafar lafiyar mata a Najeriya.
Babbar Mataimakiya ta Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Kiwon Lafiyar Mata, Dr. Adanna Steinacker, ce ta bayyana hakan a yayin taron da ta yi da ƙungiyar shugabannin mata, wakilan ƙungiyoyin mata da kungiyoyin sa-kai (NGOs) a Abuja ranar Talata.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa Ma’aikatar Kiwon Lafiya da Jin Daɗin Jama’a ta Tarayya ce ta shirya taron, tare da OSSAP-WH a matsayin mai sauƙaƙa gudanarwar sa.
Dr. Steinacker ta ce ofishinta na ɗaukar tsarin aiki na ƙasa baki ɗaya, domin tabbatar da cewa ana bai wa kiwon lafiyar mata muhimmanci a cikin tsare-tsaren ci gaban ƙasa.
A cewarta, Shugaba Bola Tinubu ne ya ƙaddamar da OSSAP-WH a ranar 11 ga Satumba, 2025, tare da ayyana aikinsa na musamman mai suna RenewHER.
Ta bayyana cewa RenewHER na nufin Health, Equity and Reform (Lafiya, Adalci da Gyara), kuma an ƙirƙire shi ne domin haɗa manufofi da tsare-tsaren kiwon lafiyar mata, tare da haɗin gwiwar Ma’aikatar Kiwon Lafiya da Ma’aikatar Harkokin Mata.
“RenewHER na da manyan ginshiƙai uku, ciki har da cibiyar kafofin watsa labarai na zamani da wayar da kai,” in ji ta.
Ta ƙara da cewa an yanke shawarar haka ne saboda gagarumin gibi na ilimi da ke akwai game da lafiyar mata da ’yan mata, tare da rashin sanin hanyoyin samun da fahimtar ayyukan kiwon lafiya da gwamnati ta tanada.
“Muna bai wa kafofin watsa labarai na zamani muhimmanci, domin yada sahihiyar bayanai da suka dogara da hujjoji, da za su ƙara fahimtar kiwon lafiya a tsakanin al’umma,” in ji ta.
Ta ce ginshiƙi na biyu na RenewHER ya shafi kamfen-kamfen da aka gina bisa yanayin yankuna, waɗanda za a aiwatar da su tare da Ma’aikatar Kiwon Lafiya, domin gano da magance manyan matsalolin lafiya a yankuna daban-daban.
“Ginshiki na uku shi ne tara haɗin gwiwar ƙungiyoyi, tarukan bita da tarukan koli, domin gina cibiyar haɗin kai da za ta inganta kiwon lafiyar mata a Najeriya,” ta ƙara da bayani.
Dr. Steinacker ta jaddada cewa Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Tarayya na da ƙudurin rushe shingayen aiki tsakanin hukumomi, tare da ɗaukar kiwon lafiyar mata a matsayin ajandar ƙasa baki ɗaya.
A nata jawabin, Sakatariyar Mandate ta Sashen Ayyukan Kiwon Lafiya da Muhalli, Dr. Adedolapo Fasawe, ta tabbatar da shirye-shiryen ofishinta na tallafa wa duk wasu tsare-tsare da za su inganta lafiyar mata da jin daɗin su.
(NAN)
