Rikicin Shugabanci: Kotun Koli ta Tabbatar da David Mark a Matsayin Shugaba

Kotun Koli ta soke umarnin “status quo ante bellum” da Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta bayar a rikicin shugabanci na jam’iyyar ADC.

Hukuncin ya dawo da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar karkashin jagorancin David Mark bayan da Independent National Electoral Commission (INEC) ta cire su daga rajista a baya.

A hukunci guda daya da alkalai biyar suka amince da shi a ranar Alhamis, kwamitin alkalai ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Lawal Garba ya bayyana cewa umarnin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayar bai zama dole ba.

Kotun Koli ta kuma bayyana cewa ƙarar da aka shigar kan batun hurumin shari’a (jurisdiction) an gabatar da ita ne kan wani umarni na gaggawa (ex parte) da ke kiran ɓangarori su bayyana dalilansu, ba tare da samun izini daga Kotun Ɗaukaka Ƙara ba.

ƙarin bayani nan gaba…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *