Aƙalla ’yan Najeriya 1,444,581 sun karɓi tabarau na karatu kyauta a ƙarƙashin shirin Gwamnatin Tarayya mai suna Effective Spectacle Coverage Initiative Nigeria (Jigi Bola 2.0), cikin shekara guda ta fara aiwatarwa.
Ministan Ƙaramar Ma’aikatar Kiwon Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Dr. Iziaq Salako, ne ya bayyana hakan a ranar Talata a Fadar Gwamnati, Abuja, yayin da yake wa manema labarai bayani a zaman farko na Meet-the-Press na shekarar 2026.
Salako ya ce shirin wani ɓangare ne na tsarin Shugaban Ƙasa na rarraba tabarau miliyan biyar kyauta ga ’yan Najeriya da ke bukata. Ana aiwatar da shirin ne ta Shirin Kula da Ido, Kunne da Sassan Ji na Ƙasa na Ma’aikatar Kiwon Lafiya, tare da haɗin gwiwar Clinton Health Access Initiative.
“Cikin shekara guda kacal na mataki na farko, mun raba fiye da tabarau miliyan 1.3, sannan mun tantance lafiyar ido ga fiye da mutane miliyan 1.5 masu shekaru 40 zuwa sama a jihohi 16,” in ji ministan. Ya bayyana shirin a matsayin ɗaya daga cikin manyan ayyukan rarraba kula da gani a Afirka.
Jihohin da ke aiwatar da shirin a halin yanzu sun haɗa da Bayelsa, Delta, Ekiti, FCT, Gombe, Imo, Kaduna, Kano, Katsina, Lagos, Plateau, Ogun, Kwara, Benue, Sokoto da Jigawa. Ya ƙara da cewa shirin ya samu kashi 94 cikin 100 na amfani da tabarau da aka bayar.
Salako ya ce kashi 65 cikin 100 na masu amfana sun karɓi tabarau na farko a rayuwarsu, yayin da mata suka kai kashi 53 cikin 100 na masu karɓa—abin da ya taimaka wajen rage gibin jinsi a samun kulawa.
Ya ce shirin ya ƙarfafa kula da lafiyar ido a matakin asibitin farko, inda aka horar da ma’aikatan lafiya 2,216, tare da kunna cibiyoyi 811 domin bayar da ayyukan asali kamar tantancewa, ba da shawara, taimakon gaggawa, rarraba tabarau, da tura marasa lafiya masu buƙatar kulawa ta gaba.
Ministan ya ƙara da cewa An sabunta Littafin Horaswa na Kula da Ido na Ƙasa, wanda yanzu ya zama ma’aunin ƙasa. Haka kuma, an tanadi cibiyoyin gani uku don sayar da tabarau a farashi mai sauƙi a Alimosho (Lagos), Ijebu-Ode (Ogun) da Idanre (Ondo).
An kuma ƙaddamar da dashbod na dijital kai-tsaye ta manhajar Kobo Collect domin bibiyar tantancewa da rarraba tabarau. Dangane da kuɗaɗe, Livelihood Impact Fund na tallafa wa ayyukan shirin tare da ɗaukar nauyin tabarau miliyan ɗaya na 2026, yayin da Founders Pledge ta ɗauki nauyin tabarau miliyan biyu, inda aka riga aka bayar da miliyan ɗaya ga ma’aikatar.
Salako ya ce ƙungiyoyin addini sun taka rawa sosai, inda Christian Health Association of Nigeria ta rarraba tabarau 201,960. Ya kawo shaidu daga masu amfana—ciki har da wani mai gyaran inji a Delta da wata likitar magunguna—da suka ce tabarau sun inganta aikinsu da rayuwarsu.
Ya sanar da cewa shirin zai faɗaɗa zuwa jihohi kamar Nasarawa, Rivers, Oyo, Enugu, Taraba, Osun, Ogun da Edo, tare da sabbin cibiyoyin gani hudu a Edo, Enugu, Nasarawa da Sokoto. Haka kuma, an sanya hannu kan yarjejeniya da Essilor Luxottica Foundation domin faɗaɗa shirin a faɗin ƙasa.
A ƙarshe, ministan ya ce shirin na maido da gani, mutunci da damar samun arziki, yana ƙarfafa tsarin lafiya na cikin gida, tare da ɗora Najeriya a sahun gaba wajen kula da lafiyar ido a Afirka, a cewarsa yana nuna ƙudurin Shugaban Ƙasa na taimaka wa ’yan Najeriya su koya, su samu abin yi, su bunƙasa, kuma su inganta rayuwarsu.
