Trends

Farashin Kaya Ya Sauka zuwa Kashi 15.1% a Watan Janairu

Hukumar Kididdiga ta Ƙasa, National Bureau of Statistics (NBS), ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki (inflation) a Najeriya ta sauka zuwa kashi 15.1 cikin ɗari a watan Janairu, daga kashi 15.15 cikin ɗari da aka samu a watan Disamban 2025.

NBS ta sanar da hakan ne a ranar Litinin yayin fitar da rahoton sabon ma’aunin farashin kayayyaki (Consumer Price Index – CPI).

A cewar hukumar, “Adadin hauhawar farashin kayayyaki na watan Janairu 2026 ya ragu da kashi 0.05 cikin ɗari idan aka kwatanta da na watan Disamban 2025.”

Ta kuma bayyana cewa, idan aka duba bisa tsarin shekara-zuwa-shekara (year-on-year), hauhawar farashin a watan Janairu 2026 ta ragu da kashi 12.51 cikin ɗari idan aka kwatanta da watan Janairu 2025, inda a wancan lokaci adadin ya kai kashi 27.61 cikin ɗari.

Hukumar ta ce hakan na nuni da cewa hauhawar farashin kayayyaki ta ragu a watan Janairu 2026 idan aka kwatanta da irin wannan lokaci a shekarar da ta gabata.

A tsarin wata-zuwa-wata (month-on-month), rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin a Janairu 2026 ta kasance -2.88 cikin ɗari, wanda ya ragu da kashi 3.42 cikin ɗari idan aka kwatanta da watan Disamba 2025 da ya kai kashi 0.54 cikin ɗari.

Wannan na nufin cewa a watan Janairu 2026, ƙarin farashin kayayyaki ya ragu idan aka kwatanta da watan Disamba 2025.

Hauhawar Farashin Abinci
Rahoton ya kuma nuna cewa hauhawar farashin abinci a watan Janairu ta kai kashi 8.89 cikin ɗari bisa tsarin shekara-zuwa-shekara.

NBS ta ce wannan adadi ya ragu da maki 20.74 idan aka kwatanta da watan Disamban 2025, wanda ya kai kashi 29.63 cikin ɗari.

A tsarin wata-zuwa-wata kuwa, hauhawar farashin abinci a Janairu 2026 ta kasance -6.02 cikin ɗari, wanda ya ragu da kashi 5.66 cikin ɗari idan aka kwatanta da Disamba 2025 (-0.36%).
Hukumar ta danganta wannan ragin da saukar farashin kayayyakin abinci kamar su doya ruwa, ƙwai, wake kore (green peas), man gyada, waken soya, man ja, masara, dawa, wake, naman sa, egusi, rogo, da farin wake.

Ta ƙara da cewa matsakaicin hauhawar farashin abinci na watanni goma sha biyu da suka ƙare a Janairu 2026 ya kai kashi 20.29 cikin ɗari, wanda ya ragu da maki 18.18 idan aka kwatanta da matsakaicin da aka samu a Janairu 2025 (38.47%).

Jihohin da Suka Fi Fuskantar Hauhawar Farashin Abinci
Rahoton ya nuna cewa a watan Janairu 2026, jihohin da suka fi fuskantar hauhawar farashin abinci bisa tsarin shekara-zuwa-shekara sun hada da Kogi (kashi 19.84%), Benue (kashi 18.38%), da Adamawa (kashi 17.29%).
A gefe guda kuma, jihohin Ebonyi (kashi 1.69%), Abia (kashi 3.23%), da Imo (kashi 3.74%) su ne suka fi samun ƙarancin hauhawar farashin abinci a wannan lokaci.

Sai dai a tsarin wata-zuwa-wata, an ce jihohin da suka fi samun canji a farashin abinci sun hada da Imo (-1.26%), Akwa Ibom (-2.21%), da Zamfara (-2.96%).
Haka kuma, jihohin Yobe (-11.88%), Nasarawa (-9.06%), da Sokoto (-8.31%) sun samu ragin farashin abinci mafi yawa a watan Janairu bisa tsarin wata-zuwa-wata.