Shugaban ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Mazi Nnamdi Kanu, ya shigar da ƙara a Kotun Ɗaukaka Ƙara kan hukuncin Kotun Tarayya da ke Abuja, wadda ta same shi da laifin ta’addanci tare da yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.
A cikin takardar ɗaukaka ƙarar da ke ɗauke da kwanan wata 4 ga Fabrairu, 2026, wadda Kanu da kansa ya sanya hannu, ya roƙi Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Abuja da ta soke hukuncin da aka yanke masa a shari’a mai lamba FHC/ABJ/CR/383/2015.
Mai ba shi shawara kan harkokin shari’a, Aloy Ejimakor, ne ya bayyana shigar da ƙarar ga manema labarai, inda ya tabbatar da cewa Kanu na neman umarnin kotu da zai soke hukuncin kotun farko tare da wanke shi daga dukkan tuhume-tuhumen da aka yi masa.
A ƙarar da ya shigar, Kanu ya sanar da kotun ɗaukaka ƙara cewa an same shi da laifin aikata ko shirya ayyukan da suka shafi ta’addanci, laifi da ke ƙarƙashin Sashe na 1(2)(b) na Dokar Hana Ta’addanci (Gyara) ta 2013, wanda hukuncinsa ya kai ɗaurin rai da rai.
Haka kuma, an same shi da laifi kan wani watsa shirye-shirye da ake zargin ya yi kusan ranar 30 ga Mayu, 2021, wanda aka ce an karɓa kuma an saurare shi a Najeriya, inda aka tuhume shi da yin barazana dangane da aiwatar da umarnin zaman gida (sit-at-home).
A cikin ƙarar tasa, Kanu ya yi iƙirarin cewa kotun sauraron ƙarar ba ta bi ka’idojin shari’a yadda ya kamata ba, yana mai cewa an yanke masa hukunci ba tare da an ba shi damar yin magana na ƙarshe (allocutus) ba, kuma kotun ba ta yi la’akari da muhimman dalilai na sassauci da na hukunci kafin ta yanke mafi tsauraran hukunci ba.
A tuna cewa a ranar 20 ga Nuwamba, 2025, Kotun Tarayya ta yanke wa Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai kan tuhume-tuhume guda bakwai na ta’addanci da suka shafi fafutukar ballewa, wanda masu gabatar da ƙara suka ce ya rikide zuwa tashin hankali a wasu sassan Kudu-maso-Gabas, Kudu-maso-Kudu, da kuma wasu yankunan jihohin Benue da Kogi.
