Cikin Jam’iyyun Siyasa 170 Masu Neman Rajista, INEC ta yi wa Biyu Kacal Rijista

Daga cikin ƙungiyoyi 171 da suka nemi a yi musu rijista a matsayin jam’iyyun siyasa, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta yi wa jam’iyya guda ɗaya kacal rijista kai tsaye, yayin da aka yi wa wata guda rijista bisa umarnin kotu.

Sabuwar jam’iyyar da ta cika dukkan sharuɗɗan doka da na tsarin mulki ita ce Democratic Leadership Alliance (DLA). Ƙungiyar Nigeria Democratic Congress (NDC) kuma an yi mata rijista ne bisa bin umarnin Kotun Tarayya da ke Lokoja, Jihar Kogi, a shari’a mai lamba FHC/LKJ/CS/49/2025, tsakanin Barrista Takori Mohammed Sanni da wasu da INEC, wadda ta umarci hukumar da ta yi wa NDC rijista a matsayin jam’iyyar siyasa.

Da yake yi wa manyan jam’iyyun siyasa daga sassan ƙasar nan bayani a Abuja a yau, 5 ga Fabrairu, Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya ce an tantance dukkan ƙungiyoyi 171 da suka mika takardun neman rajista bisa tanade-tanaden Sashe na 222 da 223 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (da aka yi wa gyara), da Sashe na 75 da 79 (1), (2) da (4) na Dokar Zaɓe ta 2022, tare da Sashe na 2 na Dokoki da Ka’idojin Jam’iyyun Siyasa na INEC na 2022.

Ya ce, “Sakamakon haka, ƙungiyoyi 14 da suka cika sharuddan farko na tantancewa aka gayyace su su wuce mataki na gaba. Daga cikinsu, guda 8 ne suka samu nasarar loda takardunsu a dandalin intanet na musamman na hukumar.”

Jam’iyyun takwas ɗin sun haɗa da All Democratic Alliance (ADA), Citizens Democratic Alliance (CDA), Abundance Social Party (ASP), African Alliance Party (AAP), Democratic Leadership Alliance (DLA), Green Future Party (GFP), National Democratic Party (NDP) da Peoples Freedom Party (PFP).
“Daga cikin waɗannan takwas, biyu ne kawai suka cancanci tantancewa da bincike na ƙarshe kan bin ka’idojin Kundin Tsarin Mulki da Dokar Zaɓe,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “Bayan cikakken nazari, jam’iyya guda ɗaya tilo—Democratic Leadership Alliance (DLA)—ce ta cika dukkan buƙatun doka gaba ɗaya.”

“Saboda haka, hukumar ta yanke shawarar yin wa Democratic Leadership Alliance (DLA) rijista a matsayin jam’iyyar siyasa, tun daga yau, 5 ga Fabrairu, 2025.”

Shugaban INEC ya kuma bayyana cewa Kotun Tarayya da ke Lokoja, Jihar Kogi, a shari’a mai lamba FHC/LKJ/CS/49/2025 tsakanin Barr. Takori Mohammed Sanni da wasu da INEC, ta umarci hukumar da ta yi wa Nigeria Democratic Congress (NDC) rijista a matsayin jam’iyyar siyasa. Ya ce hukumar ta yanke shawarar bin umarnin kotun, don haka aka yi wa jam’iyyar rijista.

Ya ce, “Za a mika takardun shaidar rajista ga sabbin jam’iyyun siyasa biyu a kan lokaci.”