Jihohin Yobe da Ogun sun samu mafi girman hauhawar farashin abinci a Najeriya, duk da cewa hauhawar farashi gaba ɗaya a ƙasar ya ragu zuwa kashi 15.15 cikin 100, a cewar sabon rahoto daga Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS).
Rahoton ya nuna cewa Yobe ta samu mafi girman hauhawar farashin abinci na shekara-shekara da kashi 15.2 cikin 100, sai Ogun da kashi 14.1 cikin 100, yayin da Babban Birnin Tarayya (FCT) ya biyo baya da kashi 13.2 cikin 100. Wasu jihohi ma sun kuma fuskanci hauhawar farashin abinci tsakanin kashi 12 zuwa 12.6 cikin 100, lamarin da ke nuna yadda matsalar ke yaduwa a sassan ƙasar.
Wannan yanayi a matakin jihohi ya sha bamban da na ƙasa baki ɗaya, inda hauhawar farashi ke ci gaba da raguwa sakamakon sassaucin farashin abinci. NBS ta danganta raguwar da aka samu da ingantattun girbi, tasirin kididdiga (base effects), da sauƙaƙewar matsalolin samar da kaya a wasu yankuna.
Hauhawar farashin abinci, wadda a da ita ce ke ja-gorantar hauhawar farashi gaba ɗaya, ta fara nuna alamun raguwa, abin da ya kawo ɗan sauƙi a matakin ƙasa.
Sai dai masana na gargadi cewa halin da jihohi ke ciki na nuna hoto mai rikitarwa, a Yobe, matsalolin tsaro da ke ci gaba da faruwa, rashin ingantattun hanyoyin sufuri, da ƙarancin damar shiga kasuwanni sun sa farashin abinci ya ci gaba da tashi.
A Ogun kuwa, kusanci da Lagos, hauhawar farashin man fetur da jigilar kaya, da kuma yawan buƙatar masu saye sun ƙara matsin lamba kan farashi. A Abuja ma, tsadar rayuwa da dogaro da abincin da ake kawo wa daga wasu yankuna sun taimaka wajen tura farashi sama.
Masana tattalin arziki sun yi gargaɗi cewa ci gaba da hauhawar farashin abinci a wasu jihohi na iya ƙara tsananta matsalar ƙarancin abinci tare da rage ƙarfin sayen kuɗi na iyalai, musamman masu ƙaramin ƙarfi. Sun jaddada cewa matsakaicin ƙididdigar ƙasa na iya ɓoye wahalhalun da jama’a ke fuskanta a wuraren da hauhawar farashi ta fi tsanani.
Masana sun kuma yi kira da a ɗauki matakan gaggawa na musamman, ciki har da ƙarfafa tsaro a yankunan noma, zuba jari a ababen more rayuwa na karkara, rage farashin sufuri, da tallafa wa samar da abinci a cikin gida. A cewarsu, waɗannan matakai ne za su tabbatar da cewa amfanin raguwar hauhawar farashi ya isa ga dukkan yankunan ƙasar.

