Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Manufofin Kuɗi da Gyaran Haraji, Taiwo Oyedele, ya yi gargadin cewa gyaran haraji na zuwa ne da wasu ƙalubale, amma ya jaddada cewa mataki ne da ba makawa domin samun ci gaba mai ɗorewa.
Oyedele ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wani taron tattaunawa (colloquium) da aka gudanar a Abuja, inda ya bayyana manyan matsalolin da ke tattare da aiwatar da gyaran, ciki har da ƙarancin amincewa da gwamnati da kuma raunin al’adar biyan haraji a Najeriya.
“Gyare-gyare ba su da sauƙi, kuma masu tsauri sun fi wahala saboda suna taɓa muradun jama’a,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, “Amincewa da gwamnati da ma cikin gwamnati kanta ya yi ƙasa ƙwarai,” yana mai jaddada cewa ‘yan Najeriya da dama ba su san irin harajin da ya kamata su biya ba.
“Yawancin ‘yan Najeriya ba su da masaniya kan harajin da ya kamata su biya, ko da a ƙarƙashin tsohuwar doka, kuma ba sa biyan su,” in ji Oyedele.
Duk da waɗannan ƙalubalen, Oyedele ya nuna kyakkyawan fata cewa gyaran zai haifar da canji mai kyau, inda ya jaddada muhimmancin jarumtaka da ƙarfi na siyasa wajen aiwatar da shi.
“Abin da muka dade muna yi a baya shi ne maganin rage zafi kawai. Bai kai mu nesa ba. Yanzu muna yin tiyata. Za ta zo da ciwo, amma ita ce hanya mafi dacewa.
“Ana buƙatar jarumtaka wajen tura wannan aiki gaba, da kuma ɗaukar haɗari, domin haɗari ne sosai,” in ji Oyedele.
A nasa bangaren, Muhammad Abdullahi, Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya goyi bayan ra’ayin Oyedele, yana mai cewa sau da yawa gyare-gyare kan gaza ne saboda rashin iya sauya hangen nesa zuwa tsayayyun tsare-tsare.
Ya yabawa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa inganta yanayin tattalin arziki a matakin kasa.
“Gaba ɗaya, ra’ayina shi ne Najeriya na samun ci gaba—irin ci gaban da ban taba gani ba a rayuwata ta balaga. Idan muka ci gaba da bin wannan tafarki har ƙarshe, kowa zai amfana,” in ji Abdullahi.
