Trends

DisCos Sun Cajin Kwastomomi Naira Biliyan 255, Sun Karɓi Naira Biliyan 210 – NERC

Kamfanonin rarraba wutar lantarki a Najeriya (DisCos) sun caji kwastomomi Naira biliyan 255.19 kan wutar da aka ba su a watan Oktoba 2025, amma sun samu damar karɓar Naira biliyan 210.92 kacal, a cewar Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC).

Rahoton NERC ya nuna cewa DisCos sun karɓi wutar lantarki daga babbar tashar ƙasa (national grid) wadda darajarta ta kai Naira biliyan 303.85, sai dai ingancin cajin kuɗi (billing efficiency) ya ragu zuwa kashi 83.99 cikin 100.

Hukumar ta danganta matsalolin da ake fuskanta da ƙarancin mita, satar wutar lantarki, da kuma raunin tsarin karɓar kuɗaɗe. Duk da gyaran farashin wuta da sauran sauye-sauyen da ake aiwatarwa, fannin wutar lantarki na ci gaba da fuskantar gibin kuɗaɗen shiga.

Kamfanin Ikeja Electricity Distribution Company ne ya fi kowa yin fice wajen aiki, inda ya samu kashi 94.36 na ingancin cajin kuɗi da kuma kashi 102.07 na ingancin karɓar kuɗaɗe (collection efficiency). Eko DisCo da Kano DisCo ma sun nuna kyakkyawan aiki, inda suka samu ingancin caji na kashi 95.71 da kashi 98.05 bi da bi.

Sai dai Jos DisCo, Kaduna DisCo da Benin DisCo sun fuskanci ƙalubale wajen karɓar kuɗaɗe. Rahoton ya nuna cewa Jos DisCo ta karɓi kashi 38.98 kacal na kuɗin da ta caji kwastomomi, yayin da Kaduna DisCo ta samu kashi 43.03.

Gibin kuɗaɗen shiga da ke ci gaba da bayyana ya haifar da damuwa game da dorewar sauye-sauyen da ake yi a fannin wutar lantarki na Najeriya. NERC ta jaddada buƙatar ƙara yawan mita, rage satar wuta, da kuma ƙarfafa bin ka’idojin kasuwanci da aka shimfiɗa wa kamfanonin rarraba wuta.

Rahoton ya ƙara da cewa fannin ya samu ingancin dawo da kuɗaɗe (recovery efficiency) na kashi 82.49, wanda ke nuna adadin kuɗin da kamfanoni suka samu daga abin da aka amince su tara. Matsakaicin farashin wutar lantarki da aka amince da shi ya kai Naira 116.25 a kowace kilowatt-hour (kWh), amma a aikace matsakaicin abin da aka karɓa ya tsaya ne a Naira 95.85 a kWh.