An Cire Sunan Maryam Sanda da Wasu Daga Jerin Afuwar Shugaba Tinubu

An cire sunan Maryam Sanda, wadda aka yanke mata hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, daga jerin wadanda aka amince da su a madogaratar afuwa ta Shugaba Bola Tinubu.

Wannan na cikin sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan Harkokin Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Laraba.

A cewar sanarwar, Tinubu ya umarci a cire sunayen wadanda aka hukunta da manyan laifuka, ciki har da satar mutane, laifukan miyagun kwayoyi, safarar mutane, zamba, da kuma mallakar ko safarar makamai marasa izini daga jerin.

Haka kuma, wadanda aka riga aka amince da su a cikin jerin tsohuwar madogarar afuwa, an rage musu hukuncin.

karin bayani nan ba da jimawa ba…