Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi afuwa ga Maryam Sanda, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bayan kotu ta same ta da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, a lokacin da suka samu rikici a cikin gida.
Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin bayani da dabarun yada labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana wannan a ranar Asabar.
Maryam Sanda, mai shekaru 37 a yanzu, ta shafe shekara shida da watanni takwas a gidan gyaran hali na tsaka-tsaki da ke Suleja kafin a sako ta.
A cewar Mista Onanuga, shugaban kasa ya yanke wannan hukunci ne bayan roko daga iyalanta, wadanda suka bayyana cewa sakin ta ya dace da muradin ‘ya’yanta biyu. Haka kuma, ya ce afuwar ta samo asali ne daga kyakkyawan halinta a gidan yari da kuma nadama da ta nuna tare da rungumar sabuwar rayuwa.
Kotun Babbar Birnin Tarayya (FCT High Court) da ke Abuja ce ta same ta da laifin kisan kai, inda alkalin kotun, Mai shari’a Yusuf Halilu, ya tabbatar da cewa Maryam ta soka wa mijinta wuka har ya mutu, kuma lauyan gwamnati ya tabbatar da hujjojin safiye fiye da shakku.
Bilyaminu Bello, wanda aka kashe, ɗa ne ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Haliru Bello.
‘Yan sanda sun fara gurfanar da Maryam a gaban kotu a watan Nuwamba 2017 bisa zargin cewa ta kashe mijinta a gidansu da ke Abuja. Shari’ar ta jinkirta sau da dama saboda neman belin da aka ki yarda da shi sau da yawa, har sai a watan Maris 2018 aka ba ta beli saboda dalilan lafiya.
Shari’ar ta ci gaba da samun tsaiko saboda bacewar wasu shaidu da kuma janyewar lauyoyinta daga kare ta. A yayin shari’ar, wasu shaidu sun bayyana yadda Maryam ta taba ƙoƙarin soka wa mijinta wuka a baya, alhali ita kuwa ta kare kanta da cewa rikici ne na cikin gida da ya rikide zuwa hatsari.
Bayan kusan shekaru biyu ana shari’a, a ranar 27 ga Janairu 2020, Mai shari’a Yusuf Halilu ya tabbatar da cewa an tabbatar da laifin ta fiye da shakku, ya kuma yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Maryam Sanda tana cikin jerin mutane 175 da Shugaba Tinubu ya yi musu afuwa ko rage musu hukunci.
A cewar Mista Onanuga, jerin sun hada da masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, masu laifukan ofis, masu laifin miyagun kwayoyi da suka nuna nadama, da wasu ‘yan kasashen waje.
“Shugaba Tinubu ya yanke shawarar yin afuwa ga mafi yawansu ne bisa rahotannin da suka nuna sun nuna nadama da kyakkyawan hali a gidan yari. Wasu kuma ya gafarta musu saboda tsufa, samun sabbin sana’o’i, ko shiga karatu a Jami’ar Open University ta Najeriya (NOUN),” in ji Onanuga.
