Shugaban cocin Citadel Global Community Church, Dokta Tunde Bakare, ya bayyana cewa ana matsa masa lamba daga manyan ’yan siyasa domin ya shiga jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).
Bakare ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin bude taron farko na Citadel School of Governance Dialogue Series mai taken “Nigeria a shekaru 65: Tunanin Tarihi da Hasashen Gaba” wanda aka gudanar a Oregun, Lagos.
Sai dai ya ce bai da niyyar shiga jam’iyyar ADC duk da matsin lambar da ake masa.
A cewarsa, wasu fitattun ’yan siyasa da suka hada da tsohon gwamna da tsohon minista daga yankin Kudu maso Yamma, sun nemi ya hada kai da jam’iyyar ADC.
Ya ce, “An dade ana matsa min lamba daga manyan mutane na siyasa in shiga ADC. Suna zuwa gidana. Har ma lokacin da nake kasashen waje, shugabannin jam’iyyar suna kiran waya suna cewa suna bukatar murya ta.”
Bakare ya kara da cewa daya daga cikin matasan abokan siyasar sa — wanda ya rike manyan mukamai a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) — ya roki ya taimaka wajen karfafa ADC.
Sai dai ya yi watsi da shawarar, inda ya ce: “Ba zan shiga ADC ba. Lokacin karshe da na ji labarin ADC, jirgi ne ya fadi da ke dauke da wannan suna. Ina musu fatan alheri domin muna bukatar karfi daga jam’iyyun adawa. Amma ba za ka haifi yaro mai suna APC ba, sannan ka nemi kashe shi da hannunka. Ba za mu sake shiga rikicin Awolowo da Akintola a Kudu maso Yamma ba,” in ji shi.
Faston wanda ya taka rawa wajen kafa jam’iyyar APC, ya kara da cewa fitowar Shugaba Bola Tinubu shugaba ta kasance ne bisa nufin Allah.
Ya ce, “Idan Allah yana so ya cire ‘emilokan,’ yana da hanyarsa. Ba za ka samu irin abin da Tinubu ya kawo ba sai da taimakon Allah.”
A nasa jawabin, babban bako a taron, Farfesa Akinjide Osuntokun, wanda tsohon jakadan Najeriya ne a kasar Jamus, ya bayyana cewa rashawa da son kabilanci su ne manyan matsalolin da ke hana Najeriya cigaba.
Ya ce, bai kamata asalin kabilar shugaban kasa ya zama matsala ba matukar gwamnati tana aiki yadda ya kamata.
“Manyan matsalolin da kasar mu ke fuskanta su ne rashawa da kabilanci. Idan akwai hanya da za a kawar da wadannan mugayen dabi’u biyu, da Najeriya za ta cigaba. Rashawa ita ce uwa ko uba ga kabilanci. Idan kudin da ake sacewa za a yi amfani da shi wajen ci gaban kasa, da Najeriya za ta fi kyau.
“Gaskiya ita ce, kasancewar Tinubu dan kabilar Yarbawa ba zai sa rayuwar talakan Yarbawa ta inganta kai tsaye ba; haka nan idan shugaban kasa dan Igbo ne, hakan ba zai wadatar da talakan Igbo ba muddin babu ci gaba,” in ji Farfesa Osuntokun.
