Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana sace ‘yan matan makarantar Chibok a shekarar 2014 a matsayin babban tabo a tarihin mulkinsa, tabon da ya ce zai kasance da shi har zuwa kabarinsa.
Jonathan ya faɗi haka ne a ranar Juma’a, yayin bikin kaddamar da littafin SCARS: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum, wanda tsohon shugaban rundunar soji, Janar Lucky Irabor, ya rubuta.
Yayin da yake yabawa Irabor bisa sadaukarwarsa ga tsaron ƙasa, Jonathan ya bayyana shi a matsayin “sojan da ya tsaya kan gaskiya, ba tare da tsoma siyasa cikin harkokin tsaro ba.”
Tsohon shugaban ƙasar ya ce mafi raɗaɗin abin da ya fuskanta a mulkinsa shi ne sace dalibai mata 276 daga makarantar gwamnati ta sakandare a Chibok, Jihar Borno.
“Take ɗin littafin ya dace ƙwarai,” in ji shi. “Ɗaya daga cikin manyan tabo a gwamnatina shi ne batun ‘yan matan Chibok. Kamar yadda Bishop Kukah ya ce, babu wani likitan kwalliya da zai iya gogewa. Tabon da zan mutu da shi ne.”
Sace ‘yan matan ya haifar da gagarumin suka daga cikin gida da waje, inda aka kaddamar da yaƙin neman ceto su ta hanyar shahararren gangamin #BringBackOurGirls. Duk da cewa wasu daga cikin daliban sun tsira ko aka ceto su, har yanzu fiye da 80 ba a san inda suke ba, bayan fiye da shekara goma.
Jonathan ya tuna cewa Boko Haram ta fara ne tun 2009 lokacin da yake mataimakin shugaban ƙasa a ƙarƙashin Marigayi Umaru Musa Yar’Adua, amma rikicin ya ƙara tsananta a lokacin mulkinsa.
“Na yi yaƙi da Boko Haram na tsawon shekaru biyar a matsayin shugaban ƙasa,” in ji shi. “Na yi tsammanin Buhari zai shawo kansu cikin sauƙi, amma har yanzu suna nan. Matsalar Boko Haram ta fi yadda ake ɗauka sauƙi.”
Ya yi kira da a sake duba dabarun yaki da ta’addanci a Najeriya, inda ya ce ana iya buƙatar haɗa dabarar ƙarfin bindiga da tattaunawa.
“Dabarar ƙwarya da sanda na iya zama hanya wajen shawo kan wannan matsalar,” in ji shi.
Jonathan ya kuma nuna damuwa kan irin makaman da Boko Haram ke amfani da su, yana mai cewa a wasu lokuta suna da kayan yaƙi fiye da na sojojin ƙasa.
“Wannan ba aikin talakawan ƙauyuka masu yunwa ba ne,” in ji shi, yana nuni da yiwuwar akwai hannun waje a cikin ƙungiyar.
A lokacin sace-sacen, gwamnatin Jonathan ta sha suka sosai kan yadda ta jinkirta bayyana wa jama’a da kuma ƙin karɓar taimakon ƙasashen waje. Kungiyoyin fararen hula sun zarge ta da rashin tsari wajen magance rikicin da kuma siyasantar da al’amarin.
Sai dai Jonathan ya kare jinkirin gwamnatinsa da cewa an yi hakan ne domin kare bayanan leƙen asiri da ake aiki da su a lokacin.
Tun daga lokacin, gwamnati ta samu damar ceto ko tattauna sakin akalla dalibai 189. Duk da haka, da yawa daga cikin waɗanda suka tsira sun fuskanci matsalolin damuwa, wariya da kuma katsewar ilimi — wasu daga cikinsu sun dawo da ‘ya’ya da aka haifa a hannun masu garkuwa.
Har yanzu gwamnatin Najeriya na jaddada cewa ceto sauran ‘yan matan Chibok da aka rage, ciki har da Leah Sharibu da sauran mutanen da ke hannun Boko Haram, ya kasance babban fifiko na ƙasa.
