Hukumar Bincike ta Ƙasa ta Amurka (FBI) ta bayyana cewa tana bayar da lada har zuwa dala $10,000 ga duk wanda ya bayar da sahihan bayanai da za su kai ga kama da kuma gurfanar da wani ɗan Najeriya mai suna Olumide Adebiyi Adediran, wanda ake nema bisa zargin aikata laifukan damfara a banki.
A cewar sanarwar da aka wallafa a shafin yanar gizon FBI a ranar Laraba, Adediran yana fuskantar tuhumar damfarar banki, damfarar takardun shaida, da damfarar kati na bashi, dangane da laifukan da ake zargin ya aikata a jihar Illinois tun daga shekarar 2001.
An bayyana cewa Adediran, wanda ya kai shekaru 56, yana amfani da sunaye daban-daban kamar Kevin Olumide Adediran, Eric O. Williams, Maxo Alexandre, Olumide Adkins, da Edward N. Anderson, yana zargin yunkurin cire kuɗaɗe daga ƙatunan bashi na bogi tare da amfani da bayanan sirri na ‘yan ƙasa Amurka wajen buɗe asusun banki da na bashi.
FBI ta ce Adediran ya tsere daga yankin Central District of Illinois a watan Disamba 2001, kwanaki kafin fara shari’arsa. Daga bisani, a ranar 2 ga Janairu, 2002, an bayar da umarnin kama shi bisa zargin karya sharuddan belinsa.
Sanarwar ta ce:
“Olumide Adebiyi Adediran ana nema saboda karya sharuddan belinsa. A watan Agusta 2001, Adediran ya shiga wani banki a Champaign, Illinois, inda ya yi ƙoƙarin karɓar kuɗaɗe daga asusun da aka samu ta hanyar katin ceki na bogi.
“Haka kuma, an zarge shi da amfani da bayanan sirri na ‘yan ƙasa Amurka wajen buɗe asusun banki da kuma asusun bashi. Adediran ya tsere daga Illinois ƙarshen watan Disamba 2001, kafin fara shari’arsa da ta shafi damfarar banki, takardun shaida, da katin bashi.
“Ranar 2 ga Janairu, 2002, kotun tarayya ta Amurka da ke Urbana, Illinois ta bayar da umarnin kama shi.”
FBI ta ƙara da cewa Adediran na da alaƙa da South Florida kuma har yanzu yana cikin jerin mutanen da ake nema ruwa a jallo.
An bayyana shi da tsayin 5’11”, nauyin 200 pounds, yana da gashi baki da idanu ruwan kasa.
“FBI tana bayar da lada har zuwa dala $10,000 ga duk wanda ya bayar da bayanai da za su kai ga kama da gurfanar da Olumide Adebiyi Adediran,” in ji hukumar.
FBI ta bukaci duk wanda ke da wani bayani game da inda yake ɓoye ya tuntuɓi ofisoshin FBI a Amurka ko kuma mafi kusa da su a jakadancin Amurka ko ofishin jakadancin ƙasashen waje.
