Tsohon Shugaban Ƙasa, Dr. Goodluck Jonathan, ya sake jaddada imanin da yake da shi kan yafiya da mantawa da abin da ya gabata, yana mai cewa ba ya rike wa kowa ƙiyayya ko da an zalunce shi.
Jonathan ya bayyana hakan ne a lokacin jana’izar Chief Audu Ogbeh da aka gudanar a Abuja ranar Laraba. Ya yabawa marigayin a matsayin mutum mai tawali’u da kuma kishin zaman lafiya.
“Chief Ogbeh ba mutum ba ne da yake neman ramuwar gayya. Ya kasance mai son ci gaba da rayuwa, yana barin duk wata magana ta baya,” in ji Jonathan.
“A wannan fanni muna da ra’ayi guda. Idan wani ya cutar da ni, sai na yafe masa. Ba na riƙe ƙiyayya. Ina ganin ya fi kyau mutum ya manta da abin da ya gabata ya ci gaba gaba,” ya ƙara da cewa.
Jonathan ya tuna yadda suka fara haɗuwa da Chief Ogbeh tun lokacin da shi Jonathan ke matsayin Mataimakin Gwamna, yayin da Ogbeh yake shugabancin jam’iyyar PDP na ƙasa. Ya ce duk da cewa ana yawan raina matsayin mataimakin gwamna, Ogbeh ya nuna masa girmamawa da ƙauna.
“Na fara saduwa da Chief Ogbeh bayan na zama mataimakin gwamna. Duk da matsayin ba a cika daraja shi ba, ya karɓe ni tamkar aboki. Duk lokacin da na je Abuja, nakan tsaya gidansa mu tattauna. Mun sha hirarraki masu muhimmanci. Hakika mutum ne mai kirki da cikar zuciya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa dangantakarsu ta ci gaba har bayan da ya zama shugaban ƙasa.
“Duk lokacin da ya ke son ganawa da ni, sai ya zo, mu tattauna tsawon lokaci—wani lokaci har awa guda—kan muhimman batutuwan ƙasa,” Jonathan ya bayyana.
A cikin jawabinsa ga ‘yan siyasa, Jonathan ya yi kira da su yi koyi da dabi’un marigayin—musamman kishin ƙasa, tawali’u, da yafiya.
“Rayuwar Chief Ogbeh tana tunatar da mu cewa shugabanci ba wai kawai iko ba ne, amma hidima, sulhu da kuma gina gada tsakanin mutane. Yayin da muke tunawa da gadonsa, ina ƙarfafa shugabannin siyasa su yi koyi da irin wannan hali,” in ji Jonathan.
An gudanar da taron jana’izar tare da halartar ‘yan uwa, abokai da masoya, wanda ya zama dama na tunawa da gudummawar da Chief Ogbeh ya bayar a matsayin ɗan siyasa, dattijo mai kishin ƙasa, da kuma jagora na haɗin kan al’umma.
