Trends

Zargin Fyade: Kotu ta Gurfanar da Malamai Mata Biyu Bisa Lalata Ɗaliba ‘yar Shekara 11

Wata kotu a Tudun Wada Zaria da ke jihar Kaduna ta gurfanar da malamai biyun a gaban Babbar Kotun Majistare a ranar Alhamis, inda ake tuhumarsu da aikata laifin lalata ta hanyar dabi’a mara kyau (lesbianism) tare da wasu malamai uku da ke cikin gudu.

Asalin Lamarin

Lauyan gwamnati, ASC Mustapha Abdulkadir, ya shaida wa kotu cewa, a ranar 11 ga Satumba, wani Yahaya Aliyu daga Tudun Jukun, Zariya, ya kai ƙara ofishin NSCDC Zariya Area Command inda ya zargi malamai biyun tare da wasu uku da ke gudu.

Ya bayyana cewa waɗanda ake tuhuma sune:

Atoyebi-Eunice Temitope (mata)

Adeyemo Damilola (mata)
da wasu guda uku da ba a kama ba.

Abdulkadir ya ce, a ranar 18 ga Satumba, lokacin da matar mai ƙara take yi wa ‘yar shekara 11 wanka
wacce ke ajin JSS-1 a makarantar ta lura cewa an ci zarafinta.

Lokacin da aka tambaye ta a gida, ɗalibar ta bayyana sunayen malamai da suka aikata laifin, inda ta ce tun daga shekarar 2023 aka fara, lokacin tana aji na 3.

Zargin Da Aka Gabatar

Ɗalibar ta bayyana cewa:

Malama Temitope (wanda aka fi sani a makarantar da sunan Mrs Okasha) ta kaita bandakin kusa da ajin 4A a lokacin hutu, inda ta sanya wani abu cikin farjinta.

Ta ƙara da cewa hakan ya faru sau uku, kuma malamar ta yi barazanar cewa idan ta faɗa wa kowa, za ta sanar da masu garkuwa da mutane su sace ta.

Hakazalika, a ranar 16 ga Satumba lokacin da makaranta ta sake buɗewa, malama Damilola ta kira yarinyar zuwa bene na sashen sakandire, inda ta kaita bandakin mata, ta kuma sanya wani abu makamancin sirinji a farjinta.

Hukuncin Kotu

Mai gabatar da ƙara ya ce waɗannan ayyuka sun saɓa wa Sashe na 259 na Dokar Hukunta Laifuka ta Jihar Kaduna, 2017.

Alkalin kotun, Babbar Majistare Rabi Hashim, ta dage shari’ar zuwa 22 ga Oktoba, 2025 don cigaba da sauraro tare da jiran shawarar doka daga Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kaduna.

Haka kuma ta bayar da umarnin a tura waɗanda ake tuhuma zuwa Gidan Gyaran Hali na Zariya har zuwa lokacin da za a sake gurfanar da su.